Rikita-Rikita: Gwamnoni 4 na APC sun daura damarar yaki da Oshiomhole

Rikita-Rikita: Gwamnoni 4 na APC sun daura damarar yaki da Oshiomhole

- Gwamnoni 4 na APC sun daura damarar yaki da Oshiomhole

- Gwamnonin sun ce Oshiomhole yana wuce goda da iri

- Gwamnonin sune na Kaduna, Zamfara, Ondo da kuma Ogun

Akalla gwamnoni hudu ne kawo yanzu suka fito fili suka wasa wukar su domin shiga yaki gadan-gadan da shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, Kwamared Adams Oshiomhole game da zabukar fitar da gwani da ake yi yanzu haka.

Rikita-Rikita: Gwamnoni 4 na APC sun daura damarar yaki da Oshiomhole
Rikita-Rikita: Gwamnoni 4 na APC sun daura damarar yaki da Oshiomhole
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dan majalisar tarayya daga Arewa ya sha da kyar a hannun matasa

Gwamnonin da muka samu labarin sun soma yin fito-na-fito da shugaban jam'iyyar dai sune Abdulaziz Yari na jihar Zamfara; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nasir El-Rufai daga Kaduna da kuma Ibikunle Amosun daga jihar Ogun.

Legit.ng ta samu cewa gwamnonin dai suna zargin shugaban jam'iyyar ne da wuce makadi da rawa a wajen rawar da ya taka a yayin gudanar da zabukan fitar da gwanin.

Kawo yanzu dai jam'iyyar ta APC ta gudanar da zabukan fitar da gwanin ta na gwamnoni da kuma Sanatoci a mafiya yawan jahohi da kuma mazabun kasar nan.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar tarayyar Najeriya a rubutawa majalisar dattawan Najeriya takarda yana neman amincewar su game da wani sabon nadi da yayi a hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance.

Mun samu cewa dai shugaban kasar ya tura sunan Mista Olanipekun Olukoyede a matsayin Sakataren hukumar ta EFCC inda yake neman su tantance shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel