Kotu ta haramtawa INEC yin kutse ga sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun

Kotu ta haramtawa INEC yin kutse ga sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun

- Kotu ta dakatar da yin wani canji ga sakamakon zaben gwamnan jihar Osun

- Mr Adeleke ne ya gabatar da takardar bukatan hakan

- Ya ce dan takarar da ya lashe zaben farko da kuri'u 245,698 ya kamata ya zama mai nasara akan wanda ya lashe zaben zagaye na biyu da kuri'u 245, 345

Kotun da aka kafa don sauraron korafe korafe kan zaben gwamnan jihar Osun, ya bayar da wani umurni ga Sanata Adeleke, na dakatar da shi daga yin kutse ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, na sake fasalin sakamakon zaben da kuma wasu bayanai da ke kunshe a cikin na'urar tantance masu kada kuri'a da sauran bayanai na zaben.

Kotun, wacce mai shari'a T.A Igoche ke jagoranta, wacce har ila yau ke dauke da mai shari'a P.A Obayi a matsayin mamba, ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Alhamis a garin Osogbo yayin zamanta, kafin fara sauraren korafe korafe.

Adeleke, wanda ya ke dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP, ta hannnun lauyansa, Mr. Nathaniel Oke (SAN), ya shigar da waga bukata ta bincike tare da sake fasalin sakamakon zaben tun gabanin fara sauraren korafe korafen.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari ta rabawa mutane 10,490 Naira miliyan 210 a jihar Kaduna

Kotu ta haramtawa INEC yin kutse ga sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun
Kotu ta haramtawa INEC yin kutse ga sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun
Asali: Depositphotos

Haka zalika Adeleke a cikin takardar, ya bukaci damar baiwa hukumar INEC umurnin fitar da gaba daya jadawalin mutanen da na'urar tantance masu kada kuri'a ta tantance a zaben, na ko wanne akwati, da kuma haramtawa INEC canja bayanan cikin na'urar, tare da takardun da aka gudanar da zaben da su.

Adeleke ya bayar da wannan takardar bukata ne da cewar shine dan takarar kujerar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP, da aka gudanar a ranar 22 ga watan Satumba, 2018 kana aka sake gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar 27 ga watan Satumba, 2028.

Wasu daga cikin bayanan da takardar ta kunsa sun hada da: "Cewar gaba daya kuri'un da dan takarar farko ya lashe zaben da su a zaben farko na ranar 22 ga watan Satumba, 2018, sun kama 245,698 yayin da a zabe na biyu aka dan takarar da ya lashe na da kuri'u 245, 345.

"Cewar dan takarar zaben farko shine wanda ya cancanci zama wanda ya lashe zaben. Sai dai a zaben da dan takara na farko ya yi nasara, ita hukumar INEC ta yanke hukuncin cewa zaben bai kammalu ba, sai an sake wani zaben zagaye na biyu."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel