Yanzu Yanzu: Mutane 19 sun mutu yayinda makiyaya ke ta harbin mutane a cikin baccinsu

Yanzu Yanzu: Mutane 19 sun mutu yayinda makiyaya ke ta harbin mutane a cikin baccinsu

- An hallaka mutane 19 a sabon harin da aka kai wani kauye a jihar Plateau

- Rahotanni sun nuna cewa makiyaya ne suka farma mutanen da harbi cikin baccinsu

- Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa jami'an tsaro basu je wajen ba har yanzu

Mutane 19 ne suka mutu yayinda wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kauyen Ariri, karamar hukumar Bassa dake jihar Plateau.

Channels TV sun ruwaito cewa makiyayan sun kai hari kauyen ne a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba cikin dare, sannan suka dunga harbin mutane yayinda suke bacci.

Yanzu Yanzu: Mutane 19 sun mutu yayinda makiyaya ke ta harbin mutane a cikin baccinsu
Yanzu Yanzu: Mutane 19 sun mutu yayinda makiyaya ke ta harbin mutane a cikin baccinsu
Asali: Depositphotos

An kuma ruwaito cewa mazauna sunyi ikirarin cewa har yanzu jami’an tsaro basu isa wurin da lamarin ya afku ba sannan kuma cewa har yanzu gawawwakin mutanen da aka kashe suna nan a tarwatse a fadin gidajen su inda aka kai hare-haren.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito maku cewa hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya zargi masu madafun iko da kuma dattawan jihar Jos na kunna wutar rikicin da ta tashi a jihar.

Buratai wanda ya samu wakilcin Agundu, ya bayyana hakan a ranar Labarai, a lokacin bizne sojoji uku da aka kashe a karamar hukumar Barikin Ladi, da aka kashe su a ranar 6 ga watan Satumba, 2018.

KU KARANTA KUMA: APC ta soke zaben fidda gwani na gwamna a Zamfara

A cewarsa, kalaman dattawan da masu madafun iko ne suka harzuka zukatan matasan da suka hadda rikici a Jos, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama wadanda basu ji ba basu gani ba, wasun su ma matafiya ne da hanya ta bi da su a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel