PDP ta nisantar da kanta daga zaben fidda gwani na jihar Kano da Kwankwaso ya jagoranta

PDP ta nisantar da kanta daga zaben fidda gwani na jihar Kano da Kwankwaso ya jagoranta

- PDP a matakin kasa, ta nisantar da kanta daga zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar Kano da ya gudana a ranar Litinin

- Hakan ya biyo bayan fitar da sanarwar dage zaben fitar da gwani na kujerar gwamnonin jihohin Kano, Imo da Legas

- Ta ce nan gaba kadan jam'iyyar za ta sanar da sabon lokacin da za a gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnonin jihohin guda 3

Majalisar zartaswa ta jam'iyyar PDP a matakin kasa, ta nisantar da kanta daga zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar Kano da ya gudana a ranar Litinin. Babban mashawarcin shugaban jam'iyyar na kasa, Shehu Yusuf Kura ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Laraba.

A cewar Kura, majalisar zartaswa ta Jam'iyyar PDP (NEC) bata da wata masaniya kan cewar za a gudanar da zaben fitar da gwani a jihar, kasancewar ta fitar da sanarwar dage zaben fitar da gwani na kujerar gwamnonin jihohin Kano, Imo da Legas.

"Majalisar zartaswa ta jam'iyyar ba ta da masaniya kan cewa magoya bayan Kwankwaso sun gudanar da zabe a jihar Kano saboda tuni jam'iyyar ta fitar da sanarwar dakatar da zabukan fitar da gwani na kujerun gwamnoni a jihohi 3."

KARANTA WANNAN: Sabuwar nasara: Rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar mayan Boko Haram a Borno

PDP ta nisantar da kanta daga zaben fidda gwani na jihar Kano da Kwankwaso ya jagoranta
PDP ta nisantar da kanta daga zaben fidda gwani na jihar Kano da Kwankwaso ya jagoranta
Asali: Twitter

Shehu Yusif ya ce ya zanta da shugaban jam'iyyar na kasa, sakatare da kuma sauran mambobin majalisar zartaswara, sun kuma bashi tabbacin cewa basu da wata masaniya na cewar an gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar.

Ya ce shelkwatar jam'iyyar na kasa ba zai amince ko yin duba ga wannan sakamakon zaben fitar da gwani da aka gudanar a jihar Kano a ranar Litinin ba, kasancewar zaben ba halastacce bane, ya sabawa hukuncin da jam'iyyar ta riga da ta yanke a baya.

Kura ya ce nan gaba kadan jam'iyyar za ta sanar da sabon lokacin da za a gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnonin jihohin guda 3.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel