Shugaban masu rinjaye a majalisa Lawan ya mallaki tikitin APC a Yobe

Shugaban masu rinjaye a majalisa Lawan ya mallaki tikitin APC a Yobe

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba ya mallaki tikitin jam’iyyar Progressives Congress (APC) domin takarar kujerar sanata a yankin Yobe ta arewa a zabe mai zuwa.

Alhaji Umar Kareto, jami’an zaben yace wakilai 1,865 aka tantance a mazabar shugaban majalisar inda ya samu kuri’u 1,702 yayinda aka soke 12.

Lawan wanda ya fito bai da abokin hamayya yayi godiya ga mutanen da suka amince da shi domin ya wakilci yankin a majalisar dattawa.

Shugaban masu rinjaye a majalisa Lawan ya mallaki tikitin APC a Yobe
Shugaban masu rinjaye a majalisa Lawan ya mallaki tikitin APC a Yobe
Asali: Depositphotos

Dan majalisan ya bukaci mutane da su tabbatar da cewa su ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’unsu a zaben 2019.

Yace yankin ya amfana sosai a lokacin gwamnatin APC fiye da shekaru 16 da PDP tayi tana mulki.

Lawan ya kuma yaba ma Gwamna Ibrahim Gaidam na Yobee kan irin shugabanci da yake gudanarwa kan tafarkin damokradiyya wanda ke inganta rayukan jama’a.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo

A baya Legit.ng ta rahoto cewa biyu daga cikin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake mulki a jihar Niger sun fadi zaben fidda gwani a kokarinsu na ganin sun koma majalisar dokokin kasar a ranar Talata, 2 ga watan Satumba.

Sanatocin biyu sun sha kaye ne a zaben fidda gwani da aka gudanar a fadin yankuna uku na jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel