Yan sanda sun kama barayin mota 3 a Kano

Yan sanda sun kama barayin mota 3 a Kano

Rundunar yan sanda a jihar Kan sun kama wasu mutane uku da ake zargin sun shahara wajen sace-sacen ababen hawa a wuraren jama’a cikin jihar.

Kakakin yan sandan jihar, SP Magaji Musa Majia ya bayyana sunayensu a matsayin Ibrahim Hamisu, Yusuf Musa da kuma Imrana Sani Bala.

Majia ya bayyana daya daga cikin masu laifin, Hamisu a matsayin gawurtaccen barawon mota wanda ya dade yana wannan aiki na sace-sacen mota.

Yan sanda sun kama barayin mota 3 a Kano
Yan sanda sun kama barayin mota 3 a Kano
Asali: Depositphotos

Yace Hamisu mazaunin Mariri quarters wanda kan ziyarci wuraren jama’a a lokutan ban mamaki sannan ya sace motocin da aka faka, an sha kama shi tare da hukunta shi akan laifin.

Majia yace da farko an kama shi aa watan Yuni sannan aka tura shi kotu domin a hukunta shi kan laifin satar mota kafin a sake kama shi a kwanan nan yana aikata wannan laifin a wajen rawa na Eleganti a hanyar filin jirgin sama.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani na APC: Gulak yayi Allah wadai da soke zaben Imo

Yace za’a tura masu laifin kotu bayan an kammala bincike.

Sannan ya shawarci masu mota a babban birnin jihar da su daina faka motocin su a wuraren da babu jama’a domin guje ma hakan musamman a lokutan da kafa suka dauke.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel