Taliyar karshe: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

Taliyar karshe: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

- Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa

- Dan majalisar daga jihar Jigawa yake

- Matasan sun ce bai yi masu komai ba

Wani dan majalisar wakilai a zauren majalisar taraya dake wakiltar mazabar Taura da Ringim a jihar Jigawa dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, Muhammad Gausu Boyi ya sha da kyar a hannun wasu mafusatan matasa.

Taliyar karshe: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa
Taliyar karshe: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sha da kyar a hannun mafusatan matasa
Asali: UGC

KU KARANTA: Wani hadimin Jonathan na neman jefa shi matsala

Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, lamarin dai ya faru ne a garin Dutse dake zaman babban birnin jihar inda dan majalisar tare da wasu magoya bayan sa suka je domin tantance su a gabanin zabukan fitar da gwani da za'a gudanar.

Legit.ng ta samu cewa sai dai isar sa farfajiyar tantancewar sai ya gamu da matasa inda suka yi masa ihu tare da fadan kalaman batanci gare shi har ma suka so su buge shi.

Amma dai da taimakon jami'an tsaron dake a wurin, hakan bata samu ba inda aka fita da shi daga wurin har sai da kura ta lafa.

A wani labarin kuma, Babban ministan harkokin cikin gida kuma mamba a majalisar zartarwar shugaba Buhari, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau ya umurci jami'an tsaron kasar nan da su lalubo hanyoyin da suka dace domin kawo karshen rikicin jihar Filato.

Dambazau, wanda ya nuna jimamin sa da da rashin jin dadi game da yadda rikicin na jihar kan lakume rayuka da dukiyoyi a duk lokacin da ya auku, ya ce dole ne a kawo karshen sa cikin gaugawa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel