Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos

Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos

- Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos

- Yace yana matukar jin kunya kan irin wannan rikici dake faruwa wanda ke ci gaba da hallaka rayuwar al’umma

- Ya roki gwamnati da tayi gaggawar daukar mataki domin magance wannan lamari da yan ta’adda ke yi

Tsohon mataimakain shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nuna bakin ciki akan rikicin baya-bayan nan da ya wakana a Jos, jihar Plateau wanda yayi sanadiyar rasa rayukan bayin Allah.

Atiku wanda ya kasance dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya nuna alhini kan lamarin a wata sanarwa a Abuja a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba inda yace yana matukar jin kunya kan irin wannan rikici dake faruwa wanda ke ci gaba da hallaka rayuwar al’umma.

Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos
Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos
Asali: Depositphotos

A cewar Atiku mutanen dake aikata wannan mumunan ta’assa sun kasance makiyan Najeeriya saboda suna haifar da yanayi mai korar masu zuba jari, wanda ke kara habbaka talauci, rashin aiki da kuma koma baya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar Kiristoci za ta tura masu sa-ido 300 a zabe mai zuwa

Ya roki gwamnati da tayi gaggawar daukar mataki domin magance wannan lamari da yan ta’adda ke yi.

Atiku ya kuma yi kira ga inganta tsaro domin taimakawa wajen gano mugun shirin da yan ta’adda ke kullawa tunda wuri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel