Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt

Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike a ranar Talata, 2 ga watan Oktoba ya gana dad an takarar shugaban kasa a PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a gidan gwamnatin Port Harcourt.

Dan takarar kujeran shugaban kasar ya isa gidan gwamnatin Port Harcourt tare da rakiyar tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Gbenga Daniel da sauran jami’an kamfen dinsa.

Gwamna Wike da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun shiga ganawa daga bisani a dakin taro na gidan gwamnatin.

Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt
Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt
Asali: Depositphotos

Atiku ya ziyarci Wike ne domin ya mika kokon bararsa ga wakilan Jam’iyyar kan su zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben fidda gwani da za’a i a karshen mako.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya mika kokon bararsa ga tawagar jam’iyyar daga jihar Katsina don su zabe shi a babban taron jam’iyyar da za’a gudanar.

KU KAARANTA KUMA: Zanga-zanga ya bata ziyarar da Saraki ya kai Kogi

Tambuwal dai na adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya kasance dan asalin jihar Katsina kuma yake neman takarar kejarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel