Rudani yayinda aka kashe mutun 1 sannan 2 na asibiti a zaben fidda gwani na APC a Bauchi

Rudani yayinda aka kashe mutun 1 sannan 2 na asibiti a zaben fidda gwani na APC a Bauchi

Rahotanni sun kawo cewa an kashe mutun daya a Boi, karamar hukumar Bogoro dake jihar Bauchi a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba yayinda yake kokarin jefa kuri’a a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) yayinda biyu ke asibiti bayan wasu mutane da ba’a sani ba sun yi harbi.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa yan takarar gwamna a APC dake takara a zaben fidda gwani, Yakubu Ibrahim Lame, da Mohammed Ali Pate sunyi zarge-zarge yayinda suke jawabi ga manema labarai a taron NUJ a yammacin ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba, kan yadda aka gudanar da shirin.

Legit.ng ta tattaro cewa su duka biyun sun sanar da janyewarsu daga shirin inda suka yi gira ga babban sakatariyar jam’iyyar ta kasa da tayi gaggawar dakatar da shirin domin a cewarsu, kwamitin sun garkame lamarin.

Rudani yayinda aka kashe mutun 1 sannan 2 na asibiti a zaben fidda gwani na APC a Bauchi
Rudani yayinda aka kashe mutun 1 sannan 2 na asibiti a zaben fidda gwani na APC a Bauchi
Asali: Twitter

Yayinda suke ci gaba da zargin cewa an hana magoya bayansu a fadin jihar zabe sunce an fesa barkonon tsohuwa sannan aka razana su domin tabbatar da cewa basu shiga shirin ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Chris Okotie ya shiga tseren neman takarar shugaban kasa

A wani lamari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda sun tarwatsa zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda bangaren Kwankwasiyya ke gudanarwa a Kano a jiya Litinin, 1 ga watan Oktoba.

Yan sanda sun hana daruruwan magoya bayan kwankwasiyya da suka taru a sakatariyar Lugard House shiga cikin ginin wanda suka yiwa kawanya tun da misalin karfe 06:00 na safe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel