Yan bindiga sun kai hari garuruwan Jos an kashe mutane 7

Yan bindiga sun kai hari garuruwan Jos an kashe mutane 7

- Mutane bakwai aka kashe bayan yan iska sun kai hari garuruwan Jos

- An rahoto cewa daya daga cikin mutanen ya kasance dalibi a jami'ar Jos

- Yan iskan sun kai hari ne dakin kwanan dalibai

Akalla mutane bakwai ne suka mutu ciki harda wani dalibin jami’ar Jos lokacin da rikici ya barke a wasu garuruwan Jos.

An rahoto cewa yan iskan sun kai hari dakin kwanan dalibai na jami’ar Jos mai suna Village Hostel, inda aka kashe wani dalibi mai suna Kums Shadrach a lokacin da suke yanke-yanken mutane.

Yan bindiga sun kai hari garuruwan Jos an kashe mutane 7
Yan bindiga sun kai hari garuruwan Jos an kashe mutane 7
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa kakakin kungiyar dalibai, Kelvin Kwalmi yace sojoji ne suka kashe Shadrach.

Legit.ng ta rahoto da farko cewa hukumar jami’ar Jos sun tabbatar da kisan dalibi daya a rikicin daya a barke a garin Jos.

Wata sanarwa daga Abdullahi Abdullahi, mataimain rijistra, bayanai da wallafe-wallafe ya bayyana cewa dalibi daya ya bata yayinda wasu biyu suka raunana.

KU KARANTA KUMA: Abin da ya sa ba zan koma Majalisar Dattawa ba - Sanata Ben Bruce

Hukumar jami’ar ace akwai bukatar tantancewa bayan bayanai daban-daban dake ta yawo musamman a shafukan zumunta kan adadin mutanen da abun ya shafa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel