Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos

Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos

- Shugaban kasa Buhari ya yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos wanda ya haddasa sanya dokar ta baci a jihar

- Da wannan ya roki daukacin al'ummar da ake wannan rikici, da su kaunci junansu da zama lafiya

- Shugaban kasar ya yi zargin cewa wasu batagarin 'yan siyasa ne ke rura wutar rikicin kabilanci dana addini don cimma wata bukata tasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos da ya barke wanda ya haddasa har gwamnatin jihar filato ta sanya dokar ta baci a wasu manyan kananan hukumomi a jihar.

Da ya ke bayyana tsantsar takaicinsa kan wannan sabon rikicin, shugaban kasa Buhari ya ce, "Hakika na damu matuka akan yadda wasu 'yan ta'adda wadanda ke biyewa zuga ta shedan suka rinka mayar da rayukan jama'a ba a bakin komai, wannan abun takaici ne."

Shugaban kasar ya tuna cewa tsawon shekaru 3 da rabi na gwamnati mai ci a yanzu a jihar, gwamnati na aiki tukuru a kowace rana tare da hadin guiwar shuwagabannin gargajiya dana addinai wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Buhari ya ce ya san cewa ba abu ne mai sauki ba, amma wahalar da mutanen Filato suka sha na gina zaman lafiya bai kamata wasu suzo su tarwatsa shi a lokaci daya ba, yana mai cewa kowanne dan kasa na da 'yancin samun kwanciyar hankalo da kuma ci gaba.

Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos
Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da sabon rikicin Jos
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Buhari ga Kumuyi: Ziyararka ta karfafa mun guiwa

"Da wannan nike rokon daukacin al'ummar jihar musamman kananan hukumomin da ake wannan rikici, da su kaunci junansu da zama lafiya. Wuraren da ake da yawan kabilu ko addinai, ko sabanin hankali, to zama a teburin sasanci shine ya fi komai wajen tabbatar da zaman lafiya.

"Ba za a iya magance matsalolin da muke fuskanta ta bangaren banbance banbancen da ke a tsakaninmu da harsashin bindiga ko sare sare da kone kone ba. Tattaunawa tare da nemo maslaha shine hanyar da doka ta tanadar," a cewar shugaban kasar.

Shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa wasu batagarin 'yan siyasa ne ke rura wutar rikicin kabilanci dana addini don cimma wata bukata tasu, duk da cewa suna sane da hakan na iya jawo salwantar rayukan jama'a ko tayar da rikicin da za a yi asarar dukiya mai tarin yawa.

Ya ce gwamnatin sa zata ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don gano bakin zaren musabbabin rikicin Filatp da kuma wasu sassa na kasar don sanin hanyoyin magance su.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel