Mataimakin gwamnan Sokoto yayi nasarar samun tikitin takarar gwamna na APC a 2019

Mataimakin gwamnan Sokoto yayi nasarar samun tikitin takarar gwamna na APC a 2019

Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmad Aliyu, ya zamo dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamna na 2019.

Da yake sanar da skamako a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba, a Sokoto, shugaban zaben fidda gwani na gwamna a jihar, Alhaji SulaimanAbuaka yace mutane hudu ne suka tsaya takara a zaben.

Legit.ng ta tattaro cewa Abubakar ya bayyanacewa kuri’u 3,606 aka kada ciin 4,600 a zaben fidda gwanin.

Mataimakin gwamnan Sokoto yayi nasarar samun tikitin takarar gwamna na APC a 2019
Mataimakin gwamnan Sokoto yayi nasarar samun tikitin takarar gwamna na APC a 2019
Asali: Depositphotos

Ya bayyana cewa Aliyu yasamu kuri’u 2,282 inda ya bige babban abokin adawarsa, Alhaji Faruk Yabo ya samu kuri’u 837 a lokacin zaben.

Abubakar ya bayyana cewa Alhaji Aubakar Gumbi ya samu kuri’u 70, yayinda Sana Abubakar Gada ya sam kuri’u 20. Shugaba ya kara da cewa kuri’u 397 ne aka soke.

KU KARANTA KUMA: Shekaru 58 da samun yanci: Buhari yayi gagarumin jawabi akan INEC, zabe na gaskiya da amana

Alhaji Ahmad ya mika godiya ga mambobin jam’iyyar da suka zabe shi yayinda yayi alkawarin fitar da su kunya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel