Muhimman abubuwa 6 da Buhari ya fadi a sakon cikar Najeriya 58 da samun yanci

Muhimman abubuwa 6 da Buhari ya fadi a sakon cikar Najeriya 58 da samun yanci

A yau 1 ga watan Oktoba, 2018 yayi daidai da cikar Najeriya shekaru 58 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Kamar ko da yaushe wannan rana na da matukar muhimmanci ga al’umman Najeriya domin tunawa da ranar da suka fara cin gashin kansu da kansu.

Don haka shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga al’umman kasar sa domin taya su murna tare da jan kunnensu akan wasu lamura.

Muhimman abubuwa 6 da Buhari ya fadi a sakon cikar Najeriya 58 da samun yanci
Muhimman abubuwa 6 da Buhari ya fadi a sakon cikar Najeriya 58 da samun yanci
Asali: UGC

Ga wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaban kasar ya zanta akai:

1. An samu ci gaba sosai kan lamarin tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar. Muna ci gaba da jajircewa don kawo karshen rikici sannan mu mayar da cikakken tsaro a arewa maso gabas.

2. Mun fara janyewa daga dogaro akan mai domin kara kaimi wajen inganta ma’adinai da harkar noma.

3. Ana nan ana kokarin ganin an kimtsa yankin Niger Delta, domin inganta rayuwar matasa a yankin domin su samarwa kansu da kasar mu makomai mai kyau.

KU KARANTA KUMA: Ranar yanci: Buhari yayi alkawarin aiki don zaman lafiya da cigaban Najeriya

4. Muna samun ci gaba sosai a yaki da cin hanci da rashawa sannan an samo kudaden jama’a da kadarorin kasa da dama da aka kasace. Wannan mumunan dabi’a da aka dunga gudanarwa a baya na sace biliyoyin naira ya kai karshe.

5. A matakin kasa da kasa, Shugaba Buhari yace Najeriya zata ci gaba da kasancewa mai da’a da mutunta kasashen duniya.

5. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zai ci gaba da aiki ba ji ba gani domin cigaban zaman lafiya, kare al’umma da kuma inganta Najeriya, ba tare da la’akari da tushe ko wariya a tsakanin al’umman kasar ba.

6. Shugaba Buhari ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da tallafawa duk shirye-shiryen da zai magance matsalolin wannan lokaci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel