2019: Gwamna Sani Bello yayi nasarar zama dan takarar gwamna na APC a Niger

2019: Gwamna Sani Bello yayi nasarar zama dan takarar gwamna na APC a Niger

- Jam'iyyar APC a Niger ta tsayar da Gwamna Abubakar Bello a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2019

- Mambobin jam’iyyar daga mazabu 274 sunyi tururuwar fitowa don tabbatar da Bello a matsayin dan takarar jam’iyyar

- Gwamnan ya nuna farin cikinsa da alkawarin ci gaba da kyawawan ayyukan da ya fara

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Niger ta tsayar da Gwamna Abubakar Bello a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2019 a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa mambobin jam’iyyar daga mazabu 274 sunyi tururuwar fitowa don tabbatar da Bello a matsayin dan takarar jam’iyyar.

2019: Gwamna Sani Bello yayi nasarar zama dan takarar gwamna na APC a Niger
2019: Gwamna Sani Bello yayi nasarar zama dan takarar gwamna na APC a Niger
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Bello, ya nuna godiyarsa ga mambobin jam’iyyar kan yarda da suka yi da shi sannan suka dawo dashi ba tare da abokin adawa ba.

Bello ya ba jam’iyyar da mutanen jihar tabbacin cewa zai sake jajircewa wajen tabbatar da kyawawan ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

A wani lamarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Tsohon shugaban EFCC, Mallam Nuhu Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamna dake gudana a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Adamawa.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an tantance Ribadu, Mahmood Halilu da gwamna Muhammadu Bindow mai ci a yanzu don su kara a zaben fidda gwani na ranar Lahadi.

Wata sanarwa daga darakta janar na kungiyar yakin neman zaben Ribadu, Mallam Salihhu Bawuro, yace Ribadu ya yanje ne bisa ga tsarin zaben fidda gwanin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel