Yanzu-yanzu: Mama Taraba ta koma jam’iyyar UDP

Yanzu-yanzu: Mama Taraba ta koma jam’iyyar UDP

Tsohuwar minister harkokin mata, Sanata Aisha Jumma Alhassan, ta sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, zuwa jam’iyyar United Democratic Party, UDP.

Sanata Jummai wacce akafi sani da Mama Taraba ta yi murabus daga kujeran minister shugaba Buhari a yau sakamakon hanata takara kujeran gwamnan jihar Taraba da jam’iyyar APC tayi.

A sakatariya jam’iyyar UDP, Mrs Alhassan ta bayyana cewa ta fita daga jam’iyyar APC ne saboda rashin adalci da akayi mata.

A ranar Juma'a ne Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce jam'iyyar ta dakatar da ministan watsa labarai, Adebayo Shittu tare da takwararsa ta ma'aikatar harkokin mata, Aisha Al-Hassan daga tsayawa takara karkashin jam'iyyar don kare martabobin da jam'iyyar ta shimfida.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

A cewar sa, tuni dokokin Nigeria suka warware komai dangane da batun yin NYSC. Dangane da ministar harkokin mata kuwa, Aosha Al-Hassan, ya ce an cireta ne saboda jam'iyyar bata gamsu da biyayyarta ba.

KU KARANTA: Mama Taraba ta yi murabus daga gwamnatin Buhari, ta fita daga APC (Karanta Wasikar)

Oshiomhole ya ce: "Mun sanar da kowa dalla dalla a lokacin da guguwar sauyin sheka ta kada, cewar APC na iya amfana daga wannan sauyin shekar ma damar za ta taimaka wajen karfafa dokokin da sharudda ga duk wanda zai tsaya takara karkashin jam'iyyar, kuma babu wanda zai tsallake su.

"Dokar zabe da kuma dokar jam'iyyar APC ta haramtawa mutum daya shiga jam'iyyun siyasa sama da daya a lokaci daya. Babzai yiyu ace kana mamban APC ba sannan a ganka tare da wani a wata jam'iyyar kana nuna soyayyarka akansa, da yawansu na nuna suna tare da APC ne bayyana amma a zukatansu 'yan PDP ne."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel