Buhari shugaban kasata ne, ba zan zage shi don banbancin jam'iyya ba - Gwamnan PDP

Buhari shugaban kasata ne, ba zan zage shi don banbancin jam'iyya ba - Gwamnan PDP

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce ba sai ya zagi Buhari ba ne zai tabbatarwa duniya shi dan PDP ne

- Gwamnan ya ce da zaran gwamnatin jihar ta kammala gina hanyar bututu na gilashi zai sahya mata sunan Buhari

- Ya yi ikirarin cewa gaba daya masoyan Buhari a jihar Ebonyi suna sonsa ne saboda kujerarsa ba wai saboda ayyukan da ya aiwatar ba

Gwamnan jihar Ebonyi, Mr. David Umahi, ya ce sam ba sai ya ci fuskar shugaban kasa Muhammadu Buhari ko zaginsa ba kafin ya nunawa duniya cewa shi mamban jam'iyyar adawa ce ta PDP.

Umahi ya bayyana hakan a ranar Juma'a a garin Abakaliki yayin wani taron tada komada na murnar zagayowar ranar da Nigeria ta samu 'yanci daga mulkin mallaka, bayan shekaru 58 daga 1 ga watan Oktoba, 1960 da kuma bikin cikar jihar shekaru 22 da kafuwa.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta sanya sunan Buhari a hanyar bututu na gilashi da ta ke ginawa mai nisan kilo mita 1 da rabi, ya kuma ce dangantakarsa da Buhari ta zarce ta siyasa.

"Ina so in bayyana cewa idan aka cire matata, har yanzu kuma har gobe Buhari ne ubangidana wanda ya zama wajibi 'yan Nigeria su girmamashi saboda matsayinsa na shugaban kasa," a cewar gwamna Umahi.

Buhari shugaban kasata ne, ba zan zage shi don banbancin jam'iyya ba - Gwamnan PDP
Buhari shugaban kasata ne, ba zan zage shi don banbancin jam'iyya ba - Gwamnan PDP
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Rikicin Jos: Ya zama tilas Buhari da Lalong su yi murabus cikin gaggawa - Jonah Jang

"A matsayin Buhari na shugaban kasa, shi ne babbar alama da kasar ke tutiya da ita, kamar yadda jihohi ke tutiya da gwamnoninsu. Kowa ya san cewa d'a Adam tara yake bai cika goma ba, ba lallai bane ace yana yin komai dai-dai, amma ya cancanci addu'a da fatan alkairi daga bakunan jama'ar Nigeria don shugabantar su.

"Na fada a baya zan kuma sake maimaitawa; ba sai na zagi shugaban kasa Buhari ba ne zan tabbatar da cewa ni dan PDP ne, yin hakan ba aikina bane a matsayin gwamnan jiha wai in rinka zagin shugaba."

Gwamna Umahi ya ce ba wai kuma hakan na nufin da cewa ya saba koyarwar jam'iyyar PDP na yin adawa ba, a'a, sai dai ya ce duk dan APC da ke a jihar Ebonyi na son kujerar shugaban kasar ne ba wai aikin da ya ke aiwatarwa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel