Rikicin Jos: Ya zama tilas Buhari da Lalong su yi murabus cikin gaggawa - Jonah Jang

Rikicin Jos: Ya zama tilas Buhari da Lalong su yi murabus cikin gaggawa - Jonah Jang

- Sanata Jonah David Jang ya bukaci shugaban kasa Buhari da gwamna Lalong da su yi murubus sakamakon rikicin Filato

- Ya bukaci matasa da kuma jama'ar jihar Filato da kowa ya tashi tsaye don kare rayuwarsa kamar yadda doka ta tanadar

- Ya ce sabon rikicin da ya barke alama ce ta gazawar gwamnatin Buhari da kuma gwamnan jihar Filato Salomon Lalong

Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta Arewa a majalisar dattijai ta kasa kuma tsohon gwamnan jihar, Jonah David Jang, ya yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Simon Lalong da su yi murabus daga ofishinsu sakamakon kisan mutane akalla 14 da ya haddasa rikicin Jos wanda aka fara tun ranar Alhamis.

Jang, wanda ya ke nemen tikitin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya ce "zai zama babban ganganci mu amincewa babban kwamandan rundunar soji ta kasa, ya ci gaba da jan ragamar harkokin tsaro na al'umar mu".

Ya bukaci matasa da kuma jama'ar jihar Filato da su kasance masu bin doka da oda, a hannu daya kuma kowa ya tashi tsaye don kare rayuwarsa da dukiyoyinsa kaar yadda dokar kasar ta tanadar.

KARANTA WANNAN: Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado

Rikicin Jos: Ya zama tilas Buhari da Lalong su yi murabus cikin gaggawa - Jonah Jang
Rikicin Jos: Ya zama tilas Buhari da Lalong su yi murabus cikin gaggawa - Jonah Jang
Asali: Depositphotos

Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai bashi shawara kan watsa labarai, Clinton Garuba, inda ya ce wannan sabon rikicin da ya barke alama ce ta gazawar gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong.

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa rikicin ya fara ne a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, a daren ranar Alhamis, inda aka kashe mata 8, maza 4. Washe garin ranar Juma'a sai wadanda rikicin ya shafa suka tayar da tarzoma inda suka rinka tare fasinjoji da ke wucewa a manyan titunan yankunan.

Sai dai a jiya Juma'a gwamnan jihar ya sanya dokar ta baci a kananan hukumomin biyu daga karfe 6 na asuba zuwa karfe 6 na yamma, wanda ake sa ran adadin wadanda suka mutu ka iya wuce mutane 12 da suka mutu tun a daren ranar Alhamis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel