Allah-kare-bala'i: Ga karin bayani game da hatsarin jirgin saman da akayi a Abuja

Allah-kare-bala'i: Ga karin bayani game da hatsarin jirgin saman da akayi a Abuja

- Ga karin bayani game da hatsarin jirgin saman da akayi a Abuja

- Rundunar sojin saman ta kafa kwamitin da zai yi binciken kwa-kwaf kan lamarin

- Shugaban kasa ya jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su

Shugaban hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadiq Abubakar ya bayyana cewa rundunar sa tuni ta kafa wani kwamitin kwararru da zai gano musabbabin da ya jaza hatsari da jiragen rundunar biyu suka yi a garin Abuja, ranar Juma'ar da ta gabata.

Allah-kare-bala'i: Ga karin bayani game da hatsarin jirgin saman da akayi a Abuja
Allah-kare-bala'i: Ga karin bayani game da hatsarin jirgin saman da akayi a Abuja
Asali: Twitter

KU KARANTA: An gano dumbin kudaden jabu a wani kango a Arewacin Najeriya

Wannan dai ya biyo bayan umurnin da shugaban kasa ya ba shugaban ma'aikata na fadar sa, Abba Kyari umurni da ya halarci jana'izar daya daga cikin matukan jirgin saman da ya rasa ransa sakamakon hatsarin.

Legit.ng dai ta samu cewa jiragen rundunar biyu ne dai suka yi hatsari a wani kauye dake a waje-wajen garin Abuja jim kadan bayan tashin su a wani atisayen da jami'an rundunar keyi akan shiri-shiren bikin zagayowar ranar da aka ba Najeriya 'yancin kanta.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Ogun dake a yankin Kudu maso yammacin Najeriya sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin kasurgumin barawo ne da kan sanya kayan sojoji tare da kwacewa jama'a kudaden su a Karamar hukumar Obafemi-Owode.

Barawon dai wanda aka ce shekarun sa kwata-kwata 23 an kama shi ne wajen karfe 8 na dare jim kadan bayan da ya kwatar wa wani tsohon soja mai suna Adeyemo Adegboyega Naira 86,000 a tsakiyar watan nan da muke ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel