2019: Ka shirya shan kaye kamar yadda ka yiwa PDP a zaben 2015 - Bafarawa ga Buhari

2019: Ka shirya shan kaye kamar yadda ka yiwa PDP a zaben 2015 - Bafarawa ga Buhari

- Bafarawa, ya shawarci Buhari da ya shirya shan kaye kamar yadda tsohon shugaban kasa - Goodluck Jonathan ya sha a zaben 2015

- A cewar sa, iko da karfin mulki ba za su taimaki shugaba wajen samun tazarce ba a zabukan kasar

- Bafarawa ya kuma roki jami'an PDP a Kaduna da su zabe shi don samun tikitin takarar shugabancin kasar

Daya daga ciki masu neman tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Attaji Dalhatu Bafarawa, ya ce karfin iko na mulki ba shine zai iya tabbatar da mai nasara a babban zaben 2019 ba tare da shawartar shugaban kasa Buhari da ya shirya shan kaye kamar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sha a zaben 2015.

Bafarawa wanda tsohon gwamnan jihar Sokoto ne daga cikin yan takara 11 da ke son samun tikitin kujerar shugaban kasa karkashin PDP a zaben 2019m ya bayyana hakan a lokacin ganawarsa da shuwagabanni dama jami'an zaben fitar da gwani na jihar Kaduna a babbar sakatariyar PDP da ke Kaduna.

A cewar mai neman tsayawa takarar kujerar shigabancin kasar, iko da karfin mulki ba za su taimaki shugaba wajen samun tazarce ba a zabukan kasar, don haka duk wata gwamnati da ta gaza aiwatar da wani aikin azo a gani, to kuwa jama'a za su tsige ta daga mulki.

KARANTA WANNAN: Wutar rikicin jam'iyyar PDP na kara ruruwa a jihar Katsina sakamakon tsayar da Yakubu Lado

2019: Ka shirya shan kaye kamar yadda ka yiwa PDP a zaben 2015 - Bafarawa ga Buhari
2019: Ka shirya shan kaye kamar yadda ka yiwa PDP a zaben 2015 - Bafarawa ga Buhari
Asali: Depositphotos

Ya ce zaben 2015 da aka gudanar ya shaidawa kowa cewa karfin iko da izza ta mulki ba za suyi tasiri wajen samun nasarar ci gaba da shugabancin mai mulki ba, don haka ma ya ce karfin ikon Buhari ba zai hana shi ficewa daga Villa a zaben 2019 ba.

Bafarawa ya kuma roki jami'an jam'iyyar da ke kada kuri'a a zaben fitar da gwani, da su zabe shi don samun tikitin takarar shugabancin kasar.

A cewar sa, a cikin shekaru 8 na zamansa gwamnan jihar Sokto, ya aiwatar da ayyuka masu tarin yawa musamman a bangaren gina jihar da kuma walwalar jama'a, wanda zai iya nunka hakan idan har aka bashi damar zama shugaban kasar Nigeria,

Da ya ke jawabi, shugaban jam'iyyar PDP nanjihar Kaduna, Hon Felix Hassan Hyet ya ce mambobin jam'iyya na jihar na sane da irin ayyukan da Bafarawa ya yi a lokacin da ya ke gwamnan jihar Sokoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel