KARIN BAYANI: Gwamnati ta sanya dokar ta baci a garuruwan Jos

KARIN BAYANI: Gwamnati ta sanya dokar ta baci a garuruwan Jos

- Gwamna Simon Bako Lalong, ya sanya dokar ta baci daga asuba zuwa faduwar rana a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu

- Dokar ta biyo bayan rikicin da ya barke a kanan hukumomin da ya jawo mutuwar akalla mutane 14 a safiyar Juma'a

- Rikicin ya tashi ne sakamakon kashe maza 5 da mata 8 a daren ranar Alhamis a sha-tale-talen Rukuba, kusa da Jos

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya sanya dokar ta baci daga asuba zuwa faduwar rana a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu biyo bayan rikicin da ya barke a kanan hukumomin da ya jawo mutuwar akalla mutane 14 a safiyar Juma'a.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Sir. Richard Tokma ya bayyana cewa: "Biyo bayan matsalar tsaro da aka samu a wasu sassa na karamar hukumar Jos ta Arewa, gwamna Simon Bako Lalnog ya amince da sanya dokar ta baci daga karfe 6 na asuba zuwa 6 na yamma a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu da ke jihar"

Sanarwar ta ce: "Yayin da gwamnati ke kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama'a, ana shawartar al'umma da su kwantar da hankulansu tare da bin dokar da aka shimfida, da kuma bayar da rahoton duk wani motsi ko wani mutum da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro."

KARIN BAYANI: Gwamnati ta sanya dokar ta baci daga asuba zuwa faduwar rana a garuruwan Jos
KARIN BAYANI: Gwamnati ta sanya dokar ta baci daga asuba zuwa faduwar rana a garuruwan Jos
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin da ya barke a wasu sassa na garin Jos a safiyar yau ya biyo bayan kashe wasu mutane 5 da kuma mata 8 a daren ranar Alhamis a sha-tale-talen Rukuba, kusa da Jos, wanda wasu 'yan ta'adda suka yi.

Wannan kisan mutanen ya janyo hargitsi yayin da al'ummar da abun ya shafa suka harzuka tare da toshe manyan hanyoyin da motoci ke wucewa inda suke dirarwa fasinjojin da ke wucewa akan hanyoyin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda na jihar, DSP Tyopev Terna, a cikin wata sanarwa ya bayyana ewa rundunar 'yan sanda sun samu kiran gaggawa don kai dauki a inda lamarin ke faruwa inda ake harbe harbe a kan titin Rukuba kusa da Otel din Kowa da ke Jos da misalin karfe 10:05 na daren Alhamis.

DSP Terna ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka a harbe harbe an garzaya da su asibitin koyarwa na jami'ar Bingham don basu kulawar gaggawa, yayin da kuma rundunar tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro suka samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan.

Wakilinmu ya bayar da rahoton cewa zuwa yanzu an samar da tsaro mai karfi a cikin garin na Jos, rikicin da ya sa aka tilasta iyaye zuwa daukar yaransu daga makarantunsu. Kasuwanci da harkoki yau da kullum sun tsaya tsak.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel