Babu wani titi da PDP ta gina tsawon shekaru 16 da ta kwashe akan mulki - Shugaba Buhari

Babu wani titi da PDP ta gina tsawon shekaru 16 da ta kwashe akan mulki - Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce daga shekara ta 1999 zuwa 2015, babu wani titi da gwamnatin PDP ta gina a Nigeria

- Ya ce idan aka sake zabarsa karo na biyu, zai tabbata ya kara kwazo wajen bunkasa kasar ta kowace fuska kamar yadda ya fara

- Buhari ya ce ya cika alkawuran da ya dauka na samar da tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa 'yan Nigeria mazauna kasar Amurka cewa daga shekara ta 1999 zuwa 2015 na gwamnatin PDP, babu wani titi da ta gina a Nigeria, duk da babu wata kungiyar da ta fito ta yi magana akan hakan.

Ya ce idan aka sake zabarsa karo na biyu, zai tabbata ya kara kwazo wajen bunkasa kasar ta kowace fuska kamar yadda ya fara.

Da ya ke jawabi ga al'ummar Nigeria mazauna kasar Amurka, daga cikin ziyarar da ya kai New York don halartar babban taron kasa da kasa na majalisar dinkin duniya UNGA73, shugaban kasar ya ce idan har aka sake bashi dama a 2019, zai tabbatar ya kara kaimi akan wanda ya nuna yanzu.

KARANTA WANNAN: Suna kirana 'Baba Go Slow' amma yanzu ina masu hanzarin su ke? - Shugaban kasa Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da 'yan Nigeria mazauna kasar Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da 'yan Nigeria mazauna kasar Amurka
Asali: Facebook

Ya buga misali da cewa a lokacin da ya ke shugabantar gidauniyar PTF, sun gina titi daga Legas zuwa Abuja zuwa Onitsa har zuwa Fatakwal, sai dai ya ce tun daga wannan lokacin har zuwa 2015 gwmanatin PDP ba ta gina wani titi mai wannan tsawon ba.

Shugaban kasa Buhari ya ce zuwa yanzu gwamnatinsa ta cika kusan mafi girman alkawuran da ta dauka a lokacin yakin zabe da suka hada da samar da tsaro a kasar, farfado da tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Babban mai tallafawa shugaban kasar ta bangaren harkokin 'yan Nigeria mazauna kasashen ketare Hon. Abike Dabiri-Erewa, ya tabbatar da wannan ganawar tsakanin 'yan Nigeria mazauna Amurka da shugaban kasar Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel