Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara

- Rundunar 'yan sanda ajihar Kwara ta samu nasarar cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a kwaryar garin Ilorin

- Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindiga kirar Pistol, kayan tsubbace-tsubbace, tabar wiwi da sauransu

- Haka zalike rundunar ta samu nasarar cafke wasu mutane biyar dake aiki a kungiyance, wadanda suka damfari mutane 6 Naira N4m

Rundunar 'yan sanda ajihar Kwara ta samu nasarar cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a kwaryar garin Ilorin, makwanni biyu bayan kama aikin sabon kwamishinan 'yan sanda na jiahr, Mr. Bolaji Fafowora.

Da yake gabatar da 'yan fashin 19 da kuma 'yan shan jinin 11 a Ilorin, jiya Larana 26 ga watan Satumba, 2018, kwamishinan 'yan sandan ya ce wadanda ake zargin sun hada da wani mutumi mai shekaru 65 da ke gyara da kera bindugu, za a gurfanar da su a gaban kotu da zaran rundunar ta kammala bincike.

Fafowora wanda ya ce wasu daga cikin yankunan da 'yan fashin ke gudanar da aika aikarsu kafin rundunar ta samu nasrar cafke su sun hada da Ogele, layin Shao, Alapata, Kangu-Olunlade, Fate, Water View da kuma Sango.

KARANTA WANNAN: New York: Uwar gidan shugaban kasa Buhari ta gabatar jawabi a taron yaki da cutar tarin fuka

Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara
Dakile ta'addanci: Rundunar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi 30 tare da 'yan shan jini a jihar Kwara
Asali: UGC

Ya kara da cewa wasu daga cikin kayayyakin da rundunar ta kwato daga hannun 'yan fashi da kuma 'yan shan jinin sun hada da bindiga kirar Pistol da ake hadawa a Nigeria, bindigar harba ka labe, kananan gatari na fada, kayan tsubbace-tsubbace, tulin tabar wiwi, manyan wayoyin na'urar rarraba wutar lantarki da kuma mashina kirar Bajaj.

Haka zalike rundunar ta samu nasarar cafke wasu mutane biyar dake aiki a kungiyance, wadanda suka damfari mutane 6 kudi har N4m. Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun kware wajen damfarar jama'a ta hanyar basu kudaden kasashen waje na bogi, yayin da su kuma zasu karbi Naira a matsayin canji.

"Suna amfani da mota kirar Mazda 323 mai dauke da lambar FUF 646 XA Kwara, wacce itama aka kwato daga hannunsu," a cewar kwamishinan yan sandan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel