Duk gwamnonin dake adawa da Karin albashin ma’aikata za su fadi zabe – Jigon NLC yayi gargadi

Duk gwamnonin dake adawa da Karin albashin ma’aikata za su fadi zabe – Jigon NLC yayi gargadi

Mista Adamu Garba, mataimakin shugaban kungiyar kwadago na Najeriya a jihar Gombe, yayi gargadin cewa duk gwamnoni dake adawa da batun kara albashin ma’aikata za su fadi zabe karo na biyu.

Garba yayi gargadin ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Gombe a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

Ya bayyana cewa kwamitin kungiyar NLC na jihar ba zata sabama shawararta na tabbatar da bin umurnin sakatariyar kasar akan yajin aiki ba, domin tursasa biyan albashin ma’aikata mafi karanci a jihar.

Duk gwamnonin dake adawa da Karin albashin ma’aikata za su fadi zabe – Jigon NLC yayi gargadi
Duk gwamnonin dake adawa da Karin albashin ma’aikata za su fadi zabe – Jigon NLC yayi gargadi
Asali: Depositphotos

“An umurci dukkanin kungiyoyin kwadago da su bayar da cikakkaen goyon bayansu akan yajin aikin kasa baki daya. Mun bukaci mambobin mu da su tabbatar da cikakken goyon bayansu,” inji Garba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wani mutumi da ya hargitsa tsarin zabe a Osun

A cewarsa NLC ta cimma nasarar fiye da kaso 90 akan Karin albashi na 2011 wanda yake N18,000.

Yace yana da yakinin cewa fafutukar zai haifar da nasara kan jami’an gwamnati dake kan aiki da wadanda suka yi ritaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng \

Asali: Legit.ng

Online view pixel