Yanzu Yanzu: Jama’ar Lagas na tafiyar kafa tsawon mita da dama yayinda aka fara yajin aiki (hoto bidiyo)

Yanzu Yanzu: Jama’ar Lagas na tafiyar kafa tsawon mita da dama yayinda aka fara yajin aiki (hoto bidiyo)

An gano jama’a na tafiya a kafa a hanyar Ipaja Road a Lagas a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba bayan kaddamar da yajin aikin gama gari da kungiyoyin kwadago suka sanar kan lamarin karin albashin ma’aikata.

Wannan mataki da kungiyar NLC ta dauka ya haifar da wahala da Karin farashin ababen hawa yayinda aka samu karancin motocin haya da zasu kai mutane inda zasu.

Yanzu Yanzu: Jama’ar Lagas na tafiyar kafa tsawon mita da dama yayinda aka fara yajin aiki (hoto bidiyo)
Yanzu Yanzu: Jama’ar Lagas na tafiyar kafa tsawon mita da dama yayinda aka fara yajin aiki
Asali: Original

Sai dai gwamnatin tarayya ta bakin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Sanata Chris Ngige, ta bayyana cewa tattaunawa da tayi na kungiyar NLC akan Karin albashi bai haifar da da mai idanu ba.

Ngige ya fadi hakan a wata sanarwa da Samuel Olowookete, daraktan labarai na ma’aikatar ya fitar a Abuja.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin sai baba ya gani a fadin kasar, saboda lamarin karin albashin ma'aikata.

KU KARANTA KUMA: Direban Aso Villa ya yi yunkurin kashe kansa saboda karancin albashi

A safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satiumba ne kungiyoyin suka fara yajin aikin a fadin kasar.

Hakan ya biyo bayan tashi baran-baran da aka yi a tattaunawar da suka kai daren jiya Laraba, 26 ga watan Satumba suna yi da gwamnatin Tarayyar akan lamarin sabon albashi mafi karanci ga ma'aikatan kasar.

Kungiyoyin da suka hada da NLC da ULC da TUC sun dauki wannan mataki ne saboda abinda suka kira gazawar gwamnati wajen sauraron kokansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel