Shugaba Buhari zai bude sabuwar matatar danyen mai a Najeriya

Shugaba Buhari zai bude sabuwar matatar danyen mai a Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen ta na bude katafariyar matatar danyen mai a cikin satin farko na watan Nuwamna mai zuwa.

Matatar man dai kamar yadda muka samu za'a gina ta ne a garin Ogbele dake a jihar Ribas kuma ana sa ran ta rika tace danyen man da ya kai ganga dubu 10 a kowace rana.

Shugaba Buhari zai bude sabuwar matatar danyen mai a Najeriya
Shugaba Buhari zai bude sabuwar matatar danyen mai a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: PDP ta soma shirin fito da dan takarar da zai kara da Buhari

Legit.ng da ta tsinkayi mai taimakawa shugaban kasa na musamman akan harkokin 'yan Neja Delta Mista Edobor Iyamu yana fadan hakan a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom a wajen wani taron masu ruwa da tsaki.

Idan dai mai karatu bai manta ba tun wajen yakin neman zabe, shugaba Buhari ya yi alkawarin gina karin matatun man fetur domin dena shigowa da tataccen man daga kasashen waje.

A wani labarin kuma, Karamin ministan sufuri a bangaren zirga-zirgar jiragen sama na kasa Sanata Hadi Sirika a firar da yayi da manema labarai ya bayyana cewa kamfanin sufurin nan na jirgin sama mallakin Najeriya watau 'Nigerian Air' da yanzu haka aka dakatar bai taba rasa masu sa hannun jari ba.

Wannan dai na zaman tamkar martani ga ministan yada labarai na gwamnatin tarayyar, Alhaji Lai Mohammed da farko ya shaidawa 'yan Najeriya cewa rashin masu saka jari ne musabbabin dalilin dakatar da kaddamar da kamfanin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel