KAI TSAYE: Mutanen garin Disu a karamar hukumar Orolu sunce ba za suyi musharaka cikin zaben ba (Bidiyo)

KAI TSAYE: Mutanen garin Disu a karamar hukumar Orolu sunce ba za suyi musharaka cikin zaben ba (Bidiyo)

A unguwuar Idiya, Ward 8, Unit 1, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Bayan wannan hari da aka kai Orolu, mazauna garin Disu sunce sun fasa kada kuri'a sakamakon cin mutuncin da akayi musu jiya. Sun bayyana cewa an hanasu fitowa daga gidajensu.

Kalli bidiyon:

Tun misalin karfe takwas na safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Satumba 2018, jami'an hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sun isa wurare bakwai da za'a karasa zaben jihar Osun.

Jami'an hukumar yan sanda da sauran jami'an tsaron sun mamaye wuraren domin tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban zaben Olusegun Agbaje ya gargadi wadanda ba kada kuri'a zasuyi ba su nisanci wajen zaben tun yanzu.

Ana gudanar da karashen zaben ne a wurare hudu:

1. Karamar hukumar Osogbo

2. Karamar hukumar Osogbo Ife ta arewa

3. Karamar hukumar Osogbo Ife ta kudu

4. Karamar hukumar Osogbo Orolu

KAI TSAYE: Komai ya kankama a karashen zaben Osun, jami'an tsaro sun mamaye wajen
KAI TSAYE: Komai ya kankama a karashen zaben Osun, jami'an tsaro sun mamaye wajen
Asali: Original

A ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC tace ba zai yiwu ta alanta dan takaran jam’iyyar PDP a matsayin zakaran zaben ba saboda tazarar da ya baiwa mai binsa bai kai yawan kuri’un da akayi wasti da su ba, saboda haka sai an sake gudanar da wani zabe a wuraren da aka samu matsala.

Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 254,699; Gboyegaa Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 254, 345, sannan Sanata Iyiola Omisore na jam’iyyar SDP ya samu kuri’u 128, 049.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel