Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN, Mr Antonio Guterres

- Sun gana ne yayin da ake ci gaba da babban taron kasa da kasa karo na 73 wanda majalisar dinkin duniya ta shirya a birnin New York

- Itama Uwar gidan shugaban kasar, Aisha Buhari na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wani taron kawo karshen yaduwar tarin fuuka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN, Mr Antonio Guterres, don tattaunawa kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi tsaro da kuma karfafa dangantakar da take tsakanin kasar Nigeria da majalisar dinkin duniyar,

Wannan ganawar tsakanin shugaban kasa Buhari da Mr. Antonio Guterres ta gudana ne a jiya Alhamis, 26 ga watan Satumba, 2018, a yayinda ake ci gaba da babban taron kasa da kasa karo na 73 wanda majalisar dinkin duniya ta shirya a birnin New York.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar malamai 1, 850 aiki a fadin jihar

A ranar Lahadi 23 ga wata ne shugaban kasar ya bar Nigeria zuwa birnin New York don halartar taron wannan shekarar mai taken: "Samar da hanyoyin da majalisar dinkin duniya za ta zama mai amfani ga jama'a: Shugabancin kasa da kasa da kuma hadaka wajen wanzar da zaman lafiya da samar da wanzuwar al'umma daya ba tare da nuna wariya ba."

Kalli hotunan ganawar shugaban kasa Buhari da Mr Antonio Guterres.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a hanyarsa ta isa dakin ganawa da Mr. Antonio Gutteres
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a hanyarsa ta isa dakin ganawa da Mr. Antonio Gutteres
Asali: Facebook

Uwar gidan shugaban kasar, Aisha Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka raka shugaban kasar zuwa birnin New York, inda itama ta gabatar da jawabi a wani taro kan yadda za a magance yaduwar cutar tarin fuka da sauran manyan cutuka da ke daukar rayukan jama'a cikin kankanin lokaci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musayar ra'ayi da Mr Antonio Gutteres
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musayar ra'ayi da Mr Antonio Gutteres
Asali: Facebook

Daga cikin manyan ayyukan da shugaban kasarnya gabatar sun hada da jawabin da ya gabatar a jiya Talata bayan bude musayar ra'ayi a taron kasa da kasar. A cikin jawabin nasa, ya jaddada kokarin Nigeria wajen samar da tsaro da zaman lafiya; dorewar bunkasar tattalin arziki; bunkasa rayuwar mata da matasa; batu kan sauyin yanayi; kare hakkokin dan Adam; da dai sauransu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musabaha da Mr Antonio Gutteres
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musabaha da Mr Antonio Gutteres
Asali: Facebook

Shugaban kasa Buhari na sanya hannu kan kundin bakin da suka ziyarci Mr Antonio Gutteres
Shugaban kasa Buhari na sanya hannu kan kundin bakin da suka ziyarci Mr Antonio Gutteres
Asali: Facebook

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel