Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku

Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku

- Alhaji Atiku Abukar ya sha alwashin gina babban filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa a jihar Anambra idan har ya zama shugaban kasa

- Atiku ya kuma ce zai tabbatar da cewa anyiwa kasar garambawul ta hanyar baiwa jihohi 'yancin cin gashin kansu

- Ya koka kan rabuwar kawunan da ake samu a kasar wanda ya zargi rashin iya shugabancin Buhari da jawo rabuwar kawunan

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma na gaba gaba a yan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abukar ya sha alwashin cewa idan har ya zama shugaban kasa, zai gina babban filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa a jihar Anambra.

Ya bayyana cewa jihar ta cancanci samun filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa don sauka wahalhalun zirga zirgar jama'ar jihar, yana mai cewa a hannu daya kuma hakan zai bunkasa tattalin arzikin jihar idan aka yi la'akari da halin da jihar take ciki yanzu.

Tsohon shugaban kasar wanda yake zantawa da jami'an da ke kad'a kuri'a a zaben fitar da gwani a jam'iyyar PDP na jihar, a garin Awka, Atiku ya kuma ce zai tabbatar da cewa anyiwa kasar garambawul ta hanyar baiwa jihohi 'yancin cin gashin kansu ta yadda za su dogara da kawunansu ba sai sun jira kasafin kudi daga gwamnatin tarayya ba.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN

Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku
Anambra zata samu filin jirage na kasa da kasa idan har na zama shugaban kasa - Atiku
Asali: Facebook

Ya koka kan rabuwar kawunan da ake samu a kasar yana mai cewa a karkashin shugabancinsa, kowace shiyya zata samu dukkanin abubuwan da take bukata ta yadda babu yadda za ayi wani kp wasu gungun mutane su yi fito na fito don a raba kasar.

"A yau kasar mu tana a makura, don ban taba ganin kasar da ke da rabuwar kawuna kamar Nigeria ba, halin da kasar take ciki a yau ya zarce yadda take bayan kammala yakin basasa wanda ya wargaza hadin kan kasar. Kuma dalilin hakan kawai saboda mun samu gwamnati wacce bata ma san me ake nufi da wanzar da hadin kan jama'a ba," a cewar Atiku.

Dan takarar shugaban kasar ya kuma shaidawa mambobin jami'iyyar Anambra cewa yana da kyakkyawan tanadi da waraka akan matsalolin da kae fuskanta a fannin rashin aikin yi, tare da cewa gwamnatinsa zata magance dukkanin matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel