Manema aikin Hukumar FRSC sun roki Gwamnatin tarayya kan kara iyakar shekarun haihuwa na daukan aiki

Manema aikin Hukumar FRSC sun roki Gwamnatin tarayya kan kara iyakar shekarun haihuwa na daukan aiki

A yayin da hukumar kula da lafiya da tsaron manyan hanyoyi ta FRSC ke ci gaba da tantance manema aikinta a fadin kasar nan, mun samu cewa wasu daga cikin manema aikin sun bayyana wata muhimmiyar buƙata ga gwamnatin tarayya.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, wasu daga cikin manema aikin hukumar sun mika kokon barar su ga gwamnatin tarayya kan sake nazari akan iyakar shekarun haihuwa na daukan aikin.

Manema aikin Hukumar FRSC sun roki Gwamnatin tarayya kan rage iyakar shekarun daukan aiki
Manema aikin Hukumar FRSC sun roki Gwamnatin tarayya kan rage iyakar shekarun daukan aiki
Asali: UGC

Wasu daga cikin manema aikin hukumar yayin ganawarsu da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a jihar Legas sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta sake nazari kan yanke iyakar shekarun haihuwa na daukar aikin hukumar daga shekaru 30 zuwa 35.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ta kayyade shekarun haihuwa da ba su wuci 30 ba ga manema aikin masu kwali na Digiri da kuma babbar Difloma.

KARANTA KUMA: Najeriya za ta bayar da gudunmuwa wajen yakar Cutar Tarin Fuka a Duniya - Buhari

Kazalika hukumar ta kayyade shekarun da ba su haura 28 ba ga manema aikin masu kwalaye na shaidar kammala karatu a kwalejan ilimi da kuma karamar Difloma.

Daya daga cikin manema aikn hukumar, Mista Samuel Ogunmolu ya bayyana cewa, muddin gwamnatin tarayya ba sake nazari da duba kan wannan lamari na shekarun haihuwa ba to kuwa ba bu shakka hukumar za ta yiwa watsi da adadin manema aikin da dama yayin tantance su sakamakon rashin cancanta ta fuskar shekarunsu da suka haura yadda aka bukata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel