Da dumi dumi: Abraham Obasanjo ya jaddada goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Buhari a 2019

Da dumi dumi: Abraham Obasanjo ya jaddada goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa Buhari a 2019

- Abraham Olujonwo Obasanjo, dan Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika

- Ya ce a shirye ya ke don baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari duk wata gudunmowa da ya ke bukata don yin tazarce a 2019

Abraham Olujonwo Obasanjo, dan tsohon shugaban kasar Nigeria, Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasikar bashi tabbacin goyon bayansa a yakin zaben tazarcensa a zaben 2019.

A cikin wasikar da ya aikawa Festus Keyamu, daraktan watsa labarai na kungiyar yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abraham Obasanjo ya ce ya yanke wannan hukuncinne a kashin kansa don goyawa Buhari baya a zaben 2019 kasancewar ya same shi a matsayin adali mai gaskiya.

Ya ce a shirye ya ke don baiwa shugaban kasar duk wata gudunmowa da ya ke bukata ba tare da tunanin ya fito daga tsatson tsohon shugaban kasa Obasanjo ba, wanda ake ganin kamar suna basa-ga-maci.

Cikakken labarin na zuwa...

KARANTA WANNAN: Gobara daga teku: Za a rufe kotuna karfe 12:00 na daren ranar Alhamis don afkawa yajin aiki

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa a karon farko Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maidawa tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo martani kan wasikar da Obasanjon ya aika masa, inda ya zayyana wasu dalilai da suka tabbatar da cewar Buhari bai cancanci ya ci gaba da shugabantar kasar ba balle ma ya tsaya takara a 2019.

Tun a watan Janairu ne Obasanjo ya aikawa Buhari da wannan wasikar, sai dai shugaban kasar bai tashi maida martani ba sai a Afrelu.

A lokacin da ya ke bayani a Bauchi wurin taron liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama shi, shugaba Buhari ya ce bai yi niyyar cewa komai ba, amma dai a lokacin Ministan Yada Labarai ya nuna muhimmancin maida amsa, inda aka yi yarjejeniyar cewa a maida amsa ta hanyar lissafa muhimman ayyukan da gwamnatin APC ta gudanar kawai, ba tare da maida martani ko rubuta sunan Obasanjo a cikin wasikar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel