Gajiya ce ta sa ni barci a zauren Majalisar Dinkin Duniya – Gwamnan Edo

Gajiya ce ta sa ni barci a zauren Majalisar Dinkin Duniya – Gwamnan Edo

- Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana dalilisa na in bacci a tarn Majalisa Dinkin Duniya

- A cewarsa tafiya da tarin ayyuka ne suka saukar masa da gajiya har yayi ikimo

- An da gano Gwamnan yana bacci a majalisar yayinda Shugaba KsaMuhammadu Buhari ke jawabi ga shugabannin duniya

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa gajiyar doguwar tafiya da kuma ayyuka ba dare ba rana ne ya sa shi barci a Zauren Majalisar Dinkin Duniya, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jawabi ga shugabannin duniya, a ranar Talata 25 ga watan Satumba a birnin New York na Amurka.

A wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Crusoe Osagie ya ce gwamnan ya gaji sosai sakamakon ayyuka, kuma cewa kowane dan adam ya san jiki da jini, zai bukaci hutu.

Gajiya ce ta sa ni barci a zauren Majalisar Dinkin Duniya – Gwamnan Edo
Gajiya ce ta sa ni barci a zauren Majalisar Dinkin Duniya – Gwamnan Edo
Asali: Depositphotos

Ya nuna rashin jin dadin sa akan yadda ake ta yada hotunan gwamna Obaseki a shafukan yanar gizo ana nuna shi ya na barci a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce ba wani abu ba ne, shiri ne da kulle-kullen da wasu suka yi, domin su bata wa gwamnan suna.

KU KARANTA KUMA: Yajin aikin gama-gari: Muna da mai na wata guda ne kacal - NNPC

Mai magana da yawun gwamnan ya ce kamata ya yi ayi la’akari da cewa ba'a cin bashin bacci donmin barci barawo ne, musamman idan ya samu wanda ya yi aiki kuma ya gaji likis.

Ya ce ya kamata a tuna irin yadda a nan gida Najeriya ba kowane gwamna ne ke aiki tukuru ya na hana idon sa barci kamar gwamnan jihar Edo, Obaseki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel