Uwargidan Buhari da yar sa sun karfafa masa gwiwa bayan jawabin da yayi a UN (hoto)

Uwargidan Buhari da yar sa sun karfafa masa gwiwa bayan jawabin da yayi a UN (hoto)

- Uwargidan Shugaba Buhari da ýar sa Halima sun karfafa masa gwiwa bayan jawabin da yayi a Majalisar Dinkin Duniya

- Gwamnan jihar Edo, Godswin Obaseki da ministan lafiya, Isaac Adewole ma sun taya shugaban kasar murna

- A ranar Talata ne Buhari yayi jawabi ga shugabannin duniya

Uwargidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha da ‘yar sa Halima sun karfafawa shugaban kasar gwiwa bayan ya kamala jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 wanda aka gudanar a birnin New York a ranar Talata, 25 ga watan Satumba.

Gwamnan jihar Edo, Godswin Obaseki da ministan lafiya, Isaac Adewole ma sun taya shugaban kasar murna kan jawabin da yayi a taron Majalisar Dinkin Duniyan.

Uwargidan Buhari da yar sa sun karfafa masa gwiwa bayan jawabin da yayi a UN (hoto)
Uwargidan Buhari da yar sa sun karfafa masa gwiwa bayan jawabin da yayi a UN
Asali: Facebook

Shugaba Buhari yayi kira ga a dauki mmataki na duk duniy kan cin hanci da rashawa, tsaro da kuma sabonta UN a jawabin nasa ga shugabannin duniya.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a

Buhari wanda ya kasance na 14 cikin wadanda suka yi Magana a ranar farko na muhawaran, ya kuma bayyana matsayar Najeriya kan lamuran kasashen duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel