Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)

Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)

Kungiyar wasu mata masu neman a shiga das u harkoki shugabanci a jihar Kano sun gudanar da gagarumin gangami.

Matan sun fito ne daga kananan hukumomin 44 dake fadin jihar Kano.

A cewar wadannan mata, maza na yi masu wayo ta hanyar amfani da addini da al`ada da kuma wasu dabaru wajen hana mata rawar gaban hantsi a harkokin siyasa musamman a arewacin kasar.

Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)
Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano
Asali: Depositphotos

Matan sun yi jeri sahu-sahu dauke da kwalayen sanarwa da ke kira ga yan’uwansu mata da sauran al`umma da su fahimci cewa ciwon `ya mace na `yan mace ne.

Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)
Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano
Asali: Depositphotos

A Najeriyar matan kan yi irin wannan gangamin a duk lokacin da guguwar babban zabe ya gabato.

Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano (hotuna)
Mata sun yi gangami game da shigar su harkar siyasa a Kano
Asali: Depositphotos

Matan sun bayyana cewa yin ganganmi irin wannan zai ba su damar ba da gudummuwa wajen tsara manufofin da suka shafi rayuwarsu.

A jihar Kano dai mata ba su da wakilci a kowane mataki kama daga majalisun kananan hukumomi zuwa majalisar dokokin jiha da kuma majalisun tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel