Osun 2018: Kada kuji tsoro wajen fitowa kwanku da kwarkwatarku don zabe na - Adeleke

Osun 2018: Kada kuji tsoro wajen fitowa kwanku da kwarkwatarku don zabe na - Adeleke

- Sanata Adeleke Ademola ya roki jama'ar jihar Osun da su fito kwansu da kwarkwatarsu ba tare da jin tsoron komai ba don zabarsa a ranar Alhamis

- A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben jihar Osun a matsayin zaben da bai kammala

- Ya yi godiya ga daukacin al'ummar jihar Osun da suka kunyata APC duk da cewa suna da karfin iko na mulkin kasar

Sanata Ademola Adeleke wanda shi ne dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar PDP, ya yi kira ga daukacin al'ummar jihar musamman kananan hukumomin da za a sake gudanar da zaben gwamnan jihar, da su fito kwansu da kwarkwatarsu ba tare da jin tsoron komai ba don zabarsa a ranar Alhamis.

A ranar Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben jihar Osun a matsayin zaben da bai kammala ba biyo bayan gaza gudanar da zabuka a wasu kananan hukumo 3 na jihar.

Haka zalika hukuncin hakan ya biyo gayan banbancin kuri'un da ke tsakanin manyan jam'iyyun da ke takarar kujerar guda biyu, jam'iyyar PDP da Apc, wanda yawan kuri'un ya gaza kai adadin yawan kuri'un da aka soke.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya za ta sayar da kamfanoni 10 na kasar don samun kudin kasafin 2018

Sanata Ademola Adeleke
Sanata Ademola Adeleke
Asali: Depositphotos

Sanatan wanda ya roki jama'ar jihar da su zabe shi a zaben ranar Alhamis din a cikin wani bidiyo, ya kuma godewa jama'ar da suka zabe shi har ya yi nasara akan jam'iyyar APC a zaben ranar Asabar da aka gudanar.

"Ina matukar godiya ga daukacin al'ummar jihar Osun da suka kunyata APC duk da cewa suna da karfin iko na mulkin kasar. Kada kai ku gaji, kuma kada ku tsorata, ina fatan za ku fito kwanku da kwarkwatarku don zabe na a ranar Alhamis.

"Ya zama wajibi a garemu baki daya, mu taru mu sake gina jihar mu don amfanar kowa da kowa, musamman ma yayanmu da ke zuwa," a cewar Adeleke a sakon da ya fitar cikin wani bidiyo a harshen yarabanci.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar Alhamis 27 ga watan Satumba ta zama ranar da za a gudanar da zabe a kananan hukumomi 3 na jihar Osun da matsalolin suka shafa, a zagaye na biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel