Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun

Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Abdulsalam Abubakar da faston Katolika, Matthew Kukah, sun shiga ganawar sirri da shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC , Farfesa Mahmud Abubakar kan zaben jihar Osun da za’a karasa ranan Alhamis.

Ganawar na cigaba da gudana a yaunzu a dakin taron Enugu Hall, Transcorp Hilton Hotel a birnin tarayya Abuja.

Zuwa yanzu bamu da cikakken bayanan ganawar.

A shekarun bayan nan, Janar AbdulSalam ya kasance mai kokarin sulhu idan aka samu matsala da tsoron rikici a zabukan Najeriya.

A shekarar 2015, kwamitinsa na zaman lafiya ne suka tilasta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zabe.

Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun
Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun
Asali: UGC

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta tantace masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019

A ranar Lahadi, 23 ga watan Satumba, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC tace ba zai yiwu ta alanta dan takaran jam’iyyar PDP a matsayin zakaran zaben ba saboda tazarar da ya baiwa mai binsa bai kai yawan kuri’un da akayi wasti da sub a, saboda haka sai an sake gudanar da wani zabe a wuraren da aka samu matsala.

Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 254,699; Gboyegaa Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 254, 345, sannan Sanata Iyiola Omisore na jam’iyyar SDP ya samu kuri’u 128, 049.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel