Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Alhamis

Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Alhamis

- Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Alhamis, 27 ga watan Augusta

- Wannan ya biyo bayan karewar wa'adin da kungiyar ta baiwa gwamnatin tarayya na cika alkawuran da ta daukarwa kungiyar

- An bukaci al'umar Nigeria da su tanadi kayan abincinsu don komai zai iya faruwa daga nan zuwa ranar

Rahotannin da muka samu a jiya Litinin, ya tabbatar mana cewa kungiyoyin kwadago dana fararen hula za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Alhamis 27 ga wannan watan, don tilasta gwamnati da ta fadi nada kiyascin kudin da za ta rinka biyan albashi mafi karanci a kasar, da kuma sanin ranar da albashin zai fara aiki.

Legit.ng ta tattaro rahoto kan cewar kungiyar ta yanke wannan hukunci ne bayan da kungiyoyin kwadago da na fararen hula da suka hada da kungiyar NLC, TUC da kuma ULCN, suka yi wani zaman gaggawa a jihar Legas don yanke hukunci matakin da za su dauka akan gwamnatin.

Ana sa ran gobe Laraba ne kungiyar za ta sanar da wannan hukunci nata a Abuja, a inda za ta warware zare da abawa na matakin da ta dauka da kuma dalilin yin hakan tare da kuma bayyana wasu bukatu da gwamnatin tarayyar za ta cika idan har ana so ta janye yajin aikin.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: FRSC ta tantance mutane 300,000 da ke neman aikin mutane 4,000 a hukumar

Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Alhamis
Kungiyar kwadago za ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ranar Alhamis
Asali: Depositphotos

Kungiyar ta kuma shawarci al'ummar NIgeria da su tanadi kayayyakin abincinsu da dukkanin kayayyakin da za su bukata, domin abubuwa da yawa za su tsaya tsak a kasar da zaran ta fara yajin aikin a fadin kasar.

A bayanin da suka gabatar jim kadan bayan fitowa daga taron gaggawar, shuwagabannin kwamitin gudanarwa na kungiyar CWC, sun ce kungiyar NLC, TUC da kuma ULC sun yanke nasu albashin mafi karanci da ya kai N65,000 kuma sun sanar da gwamnatin tarayya wannan bukata tasu, ta hannun kwamitin da aka kafa don warware al'amarin karin albashin.

Haka zalika a takardar bayan taro da kwamitin ya karanta, ya tabbatar da cewa babu wani ma'aikaci a Nigeria da zai bi wasu matakai da suka saba da bukatun uwar kungiya, tana mai cewa idan har gwamnati bata amince da karin albashi ba, to kuwa za su juya masu baya a babban zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel