Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hoto)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hoto)

- Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya

- Shugaban na Najeriya yayi Allah wadai da ta’addanci wadda ya addabi yankunan duniya

- Ya kuma yaba ma tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela kan jajircewarsa musamman wajen wanzar da zaman lafiya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela kan jajircewarsa musamman wajen wanzar da zaman lafiya, hadin kai da sasanci.

Buhari yayi magana, a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Satumba a taron kaddamar da zaman lafiya na Nelson Mandela a hedkwatar Majalisar inkin Duniya dake birnin New York.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (hotuna)
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari yayi jawabi a taron zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya
Asali: Depositphotos

A cewar sa, Najeriya ta jajirce wajen habbaka zaman lafiya da kare yancin dukkanin mata da kuma samar da wajen da zai basu damar gane cikakken martabarsu, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Yace duniyar na fuskantar tarin kalubale kamar irn rikici, sauyin yanayi, ta’addanci, talauci, safarar makamai da kuma rikici na yan hakika.

A cewarsa, akwai bukatar hadin gwiwa domin ganin anyi kokarin gina adalci, zaman lafiya, ci gaba da kuma duniya mai inganci sannan kuma a habbaka kudirorin da Mandela ya tsaya akai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel