Gwamna Shettima ya umurci masu ruwa da tsaki na APC da shirya ma shugaba Buhari kuri’u

Gwamna Shettima ya umurci masu ruwa da tsaki na APC da shirya ma shugaba Buhari kuri’u

- Gwamna Kashim Shettima ya umurci masu ruwa da tsaki na APC da su samar wa Buhari da kuri'u mafi yawa

- Shettima na martani ne ga zaben idda gwani na jam'iyyar wanda za'a gabatar

- Gwamnan jihar Bornon yace ya dauki zaben fidda gwani na ranar Alhamis da muhimmanci ba tare da la’akari da ko Buhari na da abokin hamayya ko mai dashi ba

A ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, Gwamna Kashim Shettima ya umurci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar da su koma yankunansu domin su samar da kuri’u mafi yawa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa masu ruwa da tsakin sun hada da yan majalisun dokoki na kasa da jiha, shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi, tsoffin jami’an gwamnati da masu cid a kuma jiga-jian jam’iyyar.

Gwamna Settima ya umurci masu ruwa da tsaki na APC da shirya ma shugaba Buhari kuri’u
Gwamna Settima ya umurci masu ruwa da tsaki na APC da shirya ma shugaba Buhari kuri’u
Asali: Facebook

Shettima ya bayar da umurnin ne yayinda yake rantsar da shugabannin kananan hukumomi 27 a gidan gwamnati dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnan jihar Bornon ya bayyana cewa ya dauki zaben fidda gwani na ranar Alhamis da muhimmanci ba tare da la’akari da ko Buhari na da abokin hamayya ko mai dashi ba.

KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin garkuwa da dan shugaban APC ba – Mai laifi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela kan jajircewarsa musamman wajen wanzar da zaman lafiya, hadin kai da sasanci.

Buhari yayi magana, a yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Satumba a taron kaddamar da zaman lafiya na Nelson Mandela a hedkwatar Majalisar inkin Duniya dake birnin New York.

A cewar sa, Najeriya ta jajirce wajen habbaka zaman lafiya da kare yancin dukkanin mata da kuma samar da wajen da zai basu damar gane cikakken martabarsu, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel