Yanzu-yanzu: Tashin hankali, Mai ya karewa Jirgin sama dauke da Sule Lamido, Shehu Sani a sama

Yanzu-yanzu: Tashin hankali, Mai ya karewa Jirgin sama dauke da Sule Lamido, Shehu Sani a sama

Hankalin fasinjoji kimanin 60 ya tashi a cikin jirgin saman Azman da ya nufi Abuja daga Kano a yau Litinin yayinda mai ya kare a cikin jirgin kuma suka kasa sauka har na tsawon sa’o’i.

Wani majiya wanda ke cikin jirgin ya bayyana cewa jirgin mai lamba ZQ 2332 ya bayyanawa Sahar Reporters cewa jirgin ya tashi daga Kano misalin karfe 1:20 na rana kuma ya kamata ya sauka a Abuja misalin karfe 2:05 na rana.

Yace direban jirgin ya tuntubi filin jirgin saman domin sauka amma suka fada masa kada ya sauka saboda wasu jiragen hukumar sojin saman Najeriya na atisaye a wajen.

Direban ya shiga cikin rudani har yayi niyyar komawa Kano bayan kusan awa daya a sama bai sauka ba, amma mai ya karewa jirgin.

KU KARANTA: APC ta sanya jigonta a kwana kan halartan gangamin PDP da yayI

Wasu fasinjojin suka ce sam ba zasu yarda ba sai ya sauka sauka. Hakan ya tilasta direban sauka duk da ya sabawa umurni.

Daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin sune dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Sule Lamido; Samata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, da kuma Sanata Sabo Mohammed daga Abuja.

Mai tukin jirgin ya nemi gafararsu kan jinkirin bayan sun samu nasarar sauka daga baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel