Yanzu-Yanzu: INEC ta sanar da ranar da za'ayi zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun

Yanzu-Yanzu: INEC ta sanar da ranar da za'ayi zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun

Hukumar zabe ta kasa ta bayyana sakamakon karshe na zaben gwamnan jihar Osun

- Tace ba wanda yayi nasara a zaben sai anje zagaye na biyu

- Hukumar ta INEC tace ranar Alhamis mai zuwa za'a sake fafatawa

Yanzu yanzu labarin da muke samu da majiyoyin na nuni ne da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta bayyana cewa ranar Alhamis mai zuwa watau 27 ga watan Satumbar nan da muke ciki ne zata gudanar da zagaye na biyu na zaben gwamnan jihar Osun.

Yanzu-Yanzu: INEC ta sanar da ranar da za'ayi zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun
Yanzu-Yanzu: INEC ta sanar da ranar da za'ayi zagaye na 2 na zaben gwamnan Osun
Asali: Original

KU KARANTA: Ambaliyan ruwa yaci hanyar kauyen su Jonathan

Idan ba'a manta ba hukumar zaben ta kasa dai ta bayyana sakamakon karshe na zaben gwamnan jihar Osun inda tace bai kammalu ba sai an je zagaye na biyu.

A jiya ne dai al'ummar jihar ta Osun suka kada kuri'a don zaben sabon gwamnan su da zai mulke su har ya zuwa shekaru hudu masu zuwa bayan wa'adin mulkin gwamnan nasu da zai kare nan da 'yan watanni.

Legit.ng ta samu cewa hukumar zaben ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba saboda cewa kuri'un da aka soke a zaben sun fi kuri'un tazarar dake tsakanin manyan 'yan takarar na jam'iyyar PDP da kuma APC.

Sakamakon zaben dai kamar yadda muka samu ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar adawa a jihar na PDP mai suna Sanata Ademola Adeleke 254,698 yana da kuri'u yayin da shi kuma dan takarar jam'iyya ma mulki na APC mai suna Gboyega Oyetola yana da kuri'u 254,345.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel