Hukumar raba zakka na jihar Sokoto ta bada tallafin N 7.4m ga gajiyayyu a jihar

Hukumar raba zakka na jihar Sokoto ta bada tallafin N 7.4m ga gajiyayyu a jihar

- Hukumar fidda zakka na jihar Sokoto ta bayyana cewa ta tallafa wa kiwon lafiyar tallakawa da gajiyayu da Naira miliyan 7.4 a jihar

- Shugaban hukumar Lawal Maidoki ya bayyana hakan

- Ya ce hukumar ta amince da haka ne musamman yadda gwamnatin jihar ke tallafa musu da Naira miliyan 31.5 duk wata don jin dadin marasa galihu

Shugaban hukumar fidda zakka na jihar Sokoto, Lawal Maidoki ya sanar da cewa hukumar ta tallafa wa kiwon lafiyar tallakawa da gajiyayu da Naira miliyan 7.4 a jihar.

Hukumar raba zakka na jihar Sokoto ta bada tallafin N 7.4m ga gajiyayyu a jihar
Hukumar raba zakka na jihar Sokoto ta bada tallafin N 7.4m ga gajiyayyu a jihar
Asali: Depositphotos

Maidoki ya ce hukumar ta yi na’am da hakan ne musamman yadda gwamnatin jihar ke tallafa musu da Naira miliyan 31.5 duk wata domin tallafa wa rayuwar talakawa da gajiyayu a jihar.

“A bisa wannan dalilai ne muka raba wannan kudaden wa asibitoci, kungiyoyin da muka hada hannu da su da shagunan siyar da magunguna domin tallafa wa wadanda basu da karfin samun kiwon lafiyan da suke bukata.” Inji shi

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bada tabbacin cewa zai goyi bayan fafatukar sake fasalin Najeriya har idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019.

Mista Tambuwal, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai, ya dauki alkawarin ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Juma’a, 21 ga watan Satumba yayinda yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar.

KU KARANTA KUMA: Ministan Buhari da bai yi NYSC ba ya kare kansa

A kwanakin baya ne dan takaran ya bar jam’iyyar APC zuwa PDP inda yake da niyar tsyawa takarar kujeran shugabancin kasar.

Yace kamfen dinsa ba zai fifita wutar kabilanci ba sannan kuma zai gujema bangarenci kamar yadda ake “fuskanta a gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari”.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel