Osun 2018: Dalilin da zai sa APC tayi nasara – Etteh

Osun 2018: Dalilin da zai sa APC tayi nasara – Etteh

- Tsohuwar kakakin majalisar wakilai, Patricia Etteh ta bayyana cewa tana da yakini kan cewa jam’iyyar APC ce zata lashe zaben Osun

- Patricia ta jadadda cewa APC ta shirya ma zaben sosai

- Ta kuma yi ikirarin cewa akwai zaman lafiya sosai a lamarin siyasar yankin

Wata tsohuwar kakakin majalisar wakilai, Patricia Etteh ta bayyana cewa tana da yakini kan cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce zata yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa a yau Asabar, 22 ga watan Satumba.

Etteh wacce tayi Magana da jaridar The Nation daga gidanta na Ikire, tace jam’yyar ta shirya ma zaben dari bisa dari.

Osun 2018: Dalilin da zai sa APC tayi nasara – Etteh
Osun 2018: Dalilin da zai sa APC tayi nasara – Etteh
Asali: UGC

Ta kuma bayyana cewa jam’iyya mai mulki na iya fuskantar tarin kalubale tunda akwai shahararrun yan takara da dama dake tseren.

Tsohuwar kakakin majalisar tace bata da masaniya akan batun hadewar wasu yan takara.

KU KARANTA KUMA: Ministan Buhari da bai yi NYSC ba ya kare kansa

Etteh tace bisa ga abunda ke faruwa a siyasar Ikire, akwai zaman lafiya sosai a yankin.

Legit.ng ta tattaro cewa ta kara da cewa akwai lokutan da jam’iyyu uku zuwa hudu suka yi gangami a rana guda ba tare da rikici ba. A cewarta hakan alamu ne na cewa garin na da dattaku ta fannin siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel