Zan iya kayar da Buhari kuma nayi sa’ar kasancewa dan Kano - Kwankwaso

Zan iya kayar da Buhari kuma nayi sa’ar kasancewa dan Kano - Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, SanataRabiu Kwankwaso, yace yana da karfin bige shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe.

Ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da ganin an samu zaman lafiya, matakan tsaro da kuma kayan more rayuwa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben kasa na 2019.

Ya fadi haka ne a ranar Juma’a, 21 ga watan Satumba a lokacin wani hira a Channels Television, inda yayi ikirarin cewa yana da mabiya da dama da zasu sa yayi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Zan iya kayar da Buhari kuma nayi sa’ar kasancewa dan Kano - Kwankwaso
Zan iya kayar da Buhari kuma nayi sa’ar kasancewa dan Kano - Kwankwaso
Asali: Twitter

Yace PDP ta inganta yanzu. Yayinda yake Magana akan wanda yafi cancanta, wanda yake da karfin bige shugaba mai mulki, wanda zai iya gudanar da ayyukan gwamnati bayan zabe, inda muke da zaman lafiya, daidaituwa, cigaban al’umma da sauransu – “a nawa shawarar, kana Magana ne akan Rabiu Kwankwaso,’’ inji shi.

KU KARANTA KUMA: Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

“Siyasa, kamar yanda kuka sani, gasar lambobi ce. Nayi sa’a ni dan Kano ne inda muke da jama’a mafi yawa a kasar nan idan muka bi bayanin hukumar kidudduga a kasar nan, da kuma yanki mafi sananne.

“Na kuma yi sa’ar cewa a jihar Kano, muna da mabiya da dama, mutane masu yi mana biyayya saboda sun yarda damu kuma sun yarda cewa idsn muka yi nasara, suma zasu yi nasara,’’ inji shi.

Mista Kwankwaso, wanda a halin yanzu sanata ne mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya, yace tafiyar kwankwasiyya (magoya bayansa) basu taba samun sanayya ba kamar na yau a Kano da kuma fadin Najeriya.

Wannan, inji shi, ya kasance saboda nasarori da yayi a lokacin da ya riki mukamin gwamna ta fannin kayan more rayuwa da kuma fannin ilimi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel