Sojojin Najeriya sun soma zuke ruwan garuruwan Jos suna neman gawar dan uwan su

Sojojin Najeriya sun soma zuke ruwan garuruwan Jos suna neman gawar dan uwan su

- Sojojin Najeriya sun soma zuke ruwan garuruwan Jos suna neman gawar dan uwan su

- A baya dai mun kawo maku labarin bacewar sojan

- Wasu mata kuma sun yi zanga-zanga

Dakarun sojin Najeriya tuni sun soma aikin zuke tafkunan wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Jos ta kudu dake a jihar Filato a cigaba da zurfafa binciken neman gawar dan uwan su da ya bace a kwanan baya.

Sojojin Najeriya sun soma zuke ruwan garuruwan Jos suna neman gawar dan uwan su
Sojojin Najeriya sun soma zuke ruwan garuruwan Jos suna neman gawar dan uwan su
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Mutum 10 sun mutu a ofishin jam'iyyar APC

A baya dai mun kawo maku labarin cewa wani babban jami'in rundunar sojin ta kasa mai suna Manjo Janar Idris Alkali ya bata a kan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja.

Legit.ng ta kawo maku haka zalika cewa wani labarin da muka samu na kisan da akayi wa jami'in sojan a garin na Jos da ake zargin wasu 'yan kabilar Birom ne suka yi.

Sai dai wasu mata a garuruwan da sojojin ke aikin zuke ruwan sun yi wata zanga-zangar lumana inda suka nuna rashin amincewar su da aikin domin a cewar su ruwan suna anfanar su.

A wani labarin kuma, Wasu alkaluma da muka samu daga babban ofishin jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) dake a garin Abuja, babban birnin tarayya na nuni ne da cewa akalla mutane 1,973 yanzu haka ke takarar kujerun majalisun tarayya a jam'iyyar.

Idan aka kara rarraba wadannan alkaluman, za kuma a ga cewar akalla mutane 386 ne suka sayi fom din neman takarar kujerar dan majalisar dattawa yayin da kuma mutane 1,587 suka sayi fom din yin takarar majalisar wakilai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel