Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger

Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger

- Rundunar sojin sama ta kasa (NAF) ta tura tawagar kwararrun masana kiwon lafiya daga rundunarta zuwa Zungeru

- Ana sa ran mutane 5,000 za su amfana daga wannan tallafin kiwon lafiyar

- Rundunar sojin sama ta kai wani daukin kiwon lafiya ga al'ummar garin Shinkafi, jihar Zamfara, inda mutane 4,600 suka amfana

Rundunar sojin sama ta kasa (NAF) ta tura tawagar kwararrun masana kiwon lafiya daga rundunarta zuwa Zungeru, a karamar hukumar Wushishi da ke jihar Niger, a kokarin da rundunar ta ke yi na gudanar da ayyukan jin kai ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Tallafin kiwon lafiyar wanda rundunar ta fara a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba, na gudana ne a harabar makarantar firmare ta Zungeru, inda kusan mutane 1,000 da ambaliyar ruwan ta shafa ke samun mafaka.

Ana sa ran mutane 5,000 za su amfana daga wannan tallafin kiwon lafiyar.

Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Asali: Facebook

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga rundunar sojin saman dauke da sa hannun daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na rundunar Ibikunle Daramola, inda ta ce tawagar kwararrun masana kiwon lafiyar na karkashin jagorancin Captain Azubuike Chukwuka, daraktan kiwon lafiya da bada agajin gaggawa na shalkwatar rundunar.

KARANTA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki

Sanarwar ta ce za a gudanar da tallafin kiwon lafiyar ne har tsawon kwanaki biyar, biyo bayan umurnjn da shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Sadiwue Abubakar ya bayar, a cikin kokarin rundunar na kai dauki da bada tallafi ga fararen hula wadanda wani iftila' ya shafa.

Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Asali: Facebook

Ibikunle Daramola a cikin sanarwar, ya ce: "Daga cikin bangarorin kiwon lafiya da tawagar za su bada tallafi akwai gwajin idanuwa da lafiyar jiki, gwaji da bada bada magunguna don rage zafin jikin kananan yara, tare da bada tabarau ga marasa gani sosai.

"Haka zalika rundunar za ta gudanar da kananun tiyata ga marasa lafiyar da ke bukatar hakan, da kuma bayar da gidan sauro da dai sauran tallafin kiwon lafiya da mutanen ke bukata."

Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger
Asali: Facebook

Mutane da dama ne suka amfana daga wannan tallafi tun a ranar farko, aanda hakan ya faru a gaban kwamandan runduna ta 351 ta rundunar sojin sama da ke da sansani a Minna, Kaftin Suleiman Usman da kuma kodinetan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger Mrs. Hajiya Saratu da ma shugaban karamar hukumar Wushishi, Alhaji Bashir Umar Maishanu.

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa na fannin kiwon lafiya ga al'ummar garin Shinkafi, jihar Zamfara, inda akalla mutane 4,600 ne suka amfana ta tallafin, wadanda yakin ya tada kayar baya ya dai daita su a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel