Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki

Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki

- Fadar shugaban kasa ta roki masoyan Buhari da su yi kunnen uwar shegu da kalaman Saraki

- Saraki ya koma PDP ne da zummar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Fadar shugaban kasar ta ce Saraki mugun mutum ne da zai iya aikatawa komai don daga kansa

A ranar Alhamis, fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da su yi kunnen uwar shegu ga kausasan kalaman batanci da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ya yi akan Buhari.

Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Malam Garba Shehu, ta bukaci masoyan Buhari da su nuna halin dattako tare da tofa albarkacin bakinsu cikin kyawawan kalamai.

A cewar sanarwar, fadar shugaban kasa ta zabi ta mayar da martani akan munanan kalaman batanci da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya yi akan Buhari. Saraki ya koma PDP ne da zummar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019.

KARANTA WANNAN:

Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki
Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki
Asali: Depositphotos

Fadar shugaban kasar ta ce tun fara siyasar Saraki har zuwa yanzu, ya nuna cewar Saraki mugun mutum ne da zai iya aikatawa komai don daga kansa., tana mai cewa kalaman da ya yi afani da su akan Buhari ko kare ba zai ci ba.

"Shin sai a yanzu ne ya gano cewa shugaban kasa bai san inda ya dosa ba? Sama da shekaru 3 da Sanatan ya kwashe yana aiki kafada da kafada da Buhari, abun mamaki sai yanzu ne kwatsam zai ce bai da wani kyakkyawan kudiri?

"Ko dai yana caccakar Buhari ne saboda jam'iyyar da ya koma ba ta wani abun azo a gani da zata yi yakin zabe da shi? Koma dai menene, muna baiwa magoya bayan shugaban kasar hakuri, da su yi kunnen uwar shgu da kalaman Saraki da ma na wasu batagarin yan siyasa irinsa" a cewar sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel