Wata sabuwa: An sake bankado wani ministan Buhari da ya kauce wa yin NYSC

Wata sabuwa: An sake bankado wani ministan Buhari da ya kauce wa yin NYSC

Wani ministan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake shiga matsala bayan an gano cewar bai yi bautar kasa ba, wanda hakan na iya zama barazana ga mukaminsa harma ya kuma kai shi ga zuwa gidan yari.

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu bai yi hidimar kasa ba duk da cewar ya kamala karatu daga jami’ar Ife wacce a yanzu ake kira da jami’ar yana da shekaru 25 a duniya, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Wannan lamari na Mista Shittu wanda a yanzu yake neman kujerar gwamnan jihar Oyo na zuwa ne mako daya bayan Kemi Adeosun ta yi murabus daga matsayinta na minister kudi bayan labarin mallakar takardan NYSC na bogi ya billo.

Tun daga wancan lokacin minista Shittu ya matse abin sa ya ci gaba da harkokin sa ta siyasa inda har ya kai ga zama minista Sadarwa a wannan gwamnati.

Wata sabuwa: An sake bankado wani ministan Buhari da ya kauce wa yin NYSC
Wata sabuwa: An sake bankado wani ministan Buhari da ya kauce wa yin NYSC
Asali: Depositphotos

Tun Kafin nan Shittu ya rike mukamin dan majalisar dokoki a jihar Oyo.

Sai dai kuma ba kamar irin ta ministan Kudi Kemi Adeosun da ta zarce wurin ‘yan hada-hadar buga shaidun karya ba, Minista Shittu ya fito karara cewa lallai hakan ya faru amma sai dai shi ya dauka aikin sa da ya fara yi a wancan lokaci bayan kammala jami’ar sa ta isar masa bautar kasa.

Doka ce a Najeriya da dole sai mai neman aiki ya nuna shaidar yi wa kasa bauta wato NYSC kafin a dauke shi aiki muddun ya kammala karatun sa ta digiri.

Hakan da Minista Shittu yayi zai iya kai shi zaman gidan yari na wasu lokaci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewainistan sharia na kasa, Abubakar Malami, ya amince da koarar wasu ma’aikatan hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) guda shida ta hanyar tilasta su yin ritaya tare da kakabawa wasu karin ma’aikatan hukumar biyu takunkumi bayan samun su da laifukan da suka saba da ka’idojin aikin hukumar.

KU KARANTA KUMA: Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar

Ministan ya amince da korar ma’aikatan ne bayan kwamitin bincike da hukumar NAPTIP ta kafa ya tabbatar da samun su da aikata laifuka da dama.

Batun korar ya matukar girgiza ragowar ma’aikatan hukumar, sai dai hukumar ta NAPTIP ta bayyana cewar hukuncin da ta yanke na daga cikin matakan tsaftace aiyukan hukumar da kuma cusa da’a, biyayya da girmama dokokin aiki a zukatan ma’aikatan hukumar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel