Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar

Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba ya shayar da magoya bayan jam’iyyar Progressives Congress, (APC), mamaki yayinda ya nuna rashin sanin batun ficewar kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara daga jam’iyyar.

Yakubu Dogara kamar takwaransa na majalisar dattawa, Bukola Saraki ya dade da ficewa daga jam’iyyar mai mulki zuwa babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan shirin tantance yan takaran dake neman mukami a jam’iyyar, Gwamna Abubakar yace lallai shi bashi da masaniya akan ficewar kakakin majalisar wakilai zuwa PDP a jihar Bauhi.

Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar
Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar
Asali: Twitter

Yace: “Ban san ko ya sauya sheka ba. Ya sauya? Ban sani ba amma naji ance wasu sun yankan mai fam a PDP. Amma bamu ji wani bayani daga gare shi akan sauya shekar ba. Don haka ina jira don jin hakan."

Ya kuma kara da cewa sauya shekar Dogara ba zai shafi takararshi ba a 2019.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa dalilin da yasa ya dakile tazarcensa a matsayin gwamna karkashin APC ya kasance saboda jajircewars nason hadin kai da cigaban Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Wasu jam'iyyun siyasa sun kafa sabuwar kungiyar yakar APC da PDP

Ya bayyana hakan a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a lokain kamfen dinsa inda ya yi alkawarin samar da shugabani mai ike da nagarta da zai hada kan kasar idan har aka zabe si a matsayinshugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel