Umurnin Buhari akan Adeleke ba yana nufin wanke shi ba - Hukumar yan sanda

Umurnin Buhari akan Adeleke ba yana nufin wanke shi ba - Hukumar yan sanda

Rundunar yan sandan Najeriya, a ranar Alhamis ta mayar da martani kan umurni da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na janye gayyatar Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da tayi.

Yayinda yake magana a shirin 'Good Morning Nigeria', na gidan talbijin din NTA, mai magana da yawun rundunar yan sanda, Jimoh Moshood, ya jajjada cewa umurnin shugaban kasa ba yana nufin wanke Adeleke daga laifuka da ake zarginsa da shi ba, inda yake bayyana cewa hukumar tana iya gayyatan shi a duk lokacin da ta bukace shi.

Umunin Buhari akan Adeleke ba yana nufin wanke sh ba - Hukumar yan sanda
Umunin Buhari akan Adeleke ba yana nufin wanke sh ba - Hukumar yan sanda
Asali: UGC

Ku tuna cewa a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba an zargi dan takaran a karkashin jam’iyyuar PDP a zaben gwamna da za a gudanar kwanan nan da laifin satar amsar jarabawa bayan hukumar jarabawar WAEC, ta tabbatar da cewe ya rubuta jarabawar hukumar a shekarar 1981.

Dangane da wannan ne rundunar yan sanda ke nemansa. Haka zalika, shigar Buhari cikin al’amarin a ranar Laraba ne yasa hukumar yan sandan ta janye bincike akan al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal

Amman yayinda yake mayar da martini akan umurnin Buhari na cewa kada hukumar ta gayyace shi har sai an kamala zaben jihar Osun, Jimoh ya jaddada cewa umurnin shugaban kasar bata wanke Adeleke ba daga zargi da ake yi mishi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel